Ci-da-zucin 'yan adawa ne ya kayar da su zaɓe - Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi imani ci-da-zuci ne babban abin da ya janyo taron 'yan adawar Najeriya suka sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa da ya wuce. Ya bayyana haka lokacin da ya karɓi gwamnonin jam'iyyarsa ta APC a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi. Yana cewa a daidai lokacin da jam'iyya mai mulki take aiki tuƙuru don ci gaba da mulki a zaɓukan da aka yi a baya-bayan nan, 'yan adawa suna can sun cika da ci-da-zuci. "Sun je suna ta faɗa wa masu goya musu baya a ƙasashen waje cewa, sai sun kayar da APC. Yayin zaɓen na 25 ga watan Fabrairu, ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu ya smau ƙuri'a 8,794,726. Sai Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ya samu ƙuri'a miliyan 6,984,520. Ɗan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi yana da ƙuri'a miliyan 6,101,533, yayin da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya zo na hudu da ƙuri'a miliyan 1,496,687. Shugaba Bu