Posts

Showing posts with the label dan kasa

Bankuna Za Su Fara Ba Da Katin Dan Kasa Mai Hade Da Na ATM —Pantami

Image
Gwamnatin Tarayya ta ba wa bankunan kasuwanci izinin fara ba wa abokan huldarsu katin cirar kudi na ATM da ke hade da katin shaidar dan kasa a wurin guda. Ministan Sadarwa mai barin gado, Isa Ali Pantami, ya sanar cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince bankuna su fara bayar da katin na bai-daya ba tare da sun caji kwastomomi ko sisi a kan kudin katin ATM da aka saba ba. “An ba wa bankuna izinin buga katunan Mastercard ko Visa da za su yi amfani a matsayin katin shaidar dan kasa ba tare da sun caji ’yan Najeriya karin kudi ba. “Duk mai son karbar katin banki, sai ya sanar da su cewa mai hade da katin dan kasa yake so, sai su ba shi kati daya da ya hade abubuwa biyun,” in ji Pantami. Ya bayyana cewa, Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) ta yi haka ne da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) “domin saukaka wa duk mai bukata samun katin dan kasa ta hannun bankinsa.” Da yake jawabi bayan zaman karshe na Majalisar Zartarwa ta Tarayya da gwamnatin Buhari ta gudanar, a...