Posts

Showing posts with the label Kashe kudade

Hukumar Kula Da Lafiya A Matakin Farko Ta Kano, Ta Ce Za Ta Yi Amfani Da Fasahar Sadarwa Wajen Bibiyar Kashe Kudadenta

Image
Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kano ta bayyana yin amfani da na’urorin fasahar sadarwa na zamani wajen bin diddigin ayyukan hukumar a kowane mataki. Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kano Dr. Muhammad Nasir Mahmoud ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wata manhaja mai suna Code Name Harmonized Finacial Tracking Tool wanda sashin fasahar sadarwa na hukumar ya samar. A sanarwar da jami’in yada labarai na hukumar, Maikudi Muhammed Marafa ya sanyawa hannu, Dokta Nasir ya bayyana fatansa cewa, manhajar za ta samar da hanyar da za ta taimaka wa hukumar wajen bin diddigin duk wani tsarin tafiyar da harkokin kudi na hukumar. Ya yabawa sashin fasahar sadarwar na hukumar bisa aikin  tare da bada tabbacin goyon bayansa kan sabbin abubuwa da zasu inganta ayyukan hukumar. A nasa jawabin daraktan kudi na hukumar Malam Abubakar ya bayyana makasudin samar da manhajojin da ke da manufar tattarawa, tantancewa da kuma duba duk wa...