Posts

Showing posts with the label Fetur

Zamu duba yiwuwar taimakawa Burundi da man Fetur - Buhari

Image
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ƙasar za ta duba buƙatar taimakon makamashi, musamman man fetur da gwamnatin ƙasar Burundi ta gabatar wa ƙasarsa. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adeshina ya sanya wa hannu, shugaba Buhari ya yi alƙawarin ne bayan karɓar baƙuncin ministan kuɗi , kasafi da tsare-tsare na ƙasar Burundi Audace Niyonzima a fadarsa da ke Abuja. Sanarwar ta ce Buhari ya tabbatar wa da mista Niyonzima cewa Najeriya za ta taimaka wa ƙasar Burundi ta hanyoyi da dama ƙarƙashin inuwar zumunci da 'yan uwantaka da ke tsakanin ƙasashen Afirka. Shugaba Buhari ya ƙara da cewa ya san yadda ƙasa ke ji musamman idan tana fama da ƙarancin makamashi, tare da alƙawarta cewa zai tura batun ga babban kamfanin mai na ƙasar NNPC domin duba buƙatar. Buhari ya ce a yanzu batun zaɓen ƙasar, da batun saukarsa daga mulki ne a gabansa, tun da dai ya yi wa'adi biyu da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi dama. A nasa ɓangare ministan na Burundi ...

Sojojin haya sun kama jirgi maƙare da fetur na sata a Neja-Delta

Image
Kamfanonin tsaro biyu da Najeriya ta bai wa kwangilar tsaron bututan man fetur sun kama jiragen ruwa da mota maƙare da man da hukumomi suka ce na sata ne a yankin Neja-Delta da ke kudancin ƙasar. Wata sanarwa da kamfanin mai na Najeriya, NNPC Limited, ya fitar a yau Asabar ta tabbatar mutum huɗu aka kama yayin samamen. Kamfanin ya samu rahoton sirri game da ayyukan mutanen tun a ranar 22 ga watan Disamba. Dakarun tsaro sun isa wurin kuma suka tarar da su suna jigilar man ta ɓarauniyar hanya tare da tace gas a wata matata da ke Agge. Tuni hukumomi suka ƙona jirgin da kayan da yake ɗauke da shi. NNPC Copyright: NNPC A tsakiyar shekarar 2022 ne gwamnatin Najeriya ta ƙulla yarjejeniya da kamfanonin Tantita Security Services da zimmar daƙile ayyukan ɓarayi da kuma masu fasa bututan mai a yankin na Neja-Delta. Satar mai na jawo wa Najeriya asarar biliyoyin kuɗin shiga kuma ya sa ba ta iya haƙowa da fitar da ganga miliyan 1.8 da ƙungiyar Opec ta masu arzikin man fetur ta ƙayyade mata a kowace...