Posts

Showing posts with the label Mauritaniya

Buhari Zai Karbo Kyautar wanzar da zaman lafiya a Mauritaniya

Image
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata mai zuwa zai karbi kyautar “Karfafa zaman lafiya ta Afirka” a birnin Nouakchott na kasar Mauritaniya. Kakakin Shugaban, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi, inda ya ce Buharin zai karbi kyautar ce saboda irin rawar da yake takawa wajen wanzar da zaman lafiya da kuma yin sulhu a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka. Noman masara zai yi wahala a damina mai zuwa — Kamilu Sigau Ko sanyi na da alaka da yawaitar tashin aljanu da iskokai? Kwamitin Zaman Lafiya na Abu Dhabi, ne dai zai gabatar wa Buhari kyautar. An kafa kwamitin na Shugabannin Kasashe ne a shakara ta 2014 domin a lalubo hanyoyin bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya. Adesina ya kuma ce gabanin Buharin ya karbi kyautar, Shugaban zai halarci taron kasashen Afirka kan samar da zaman lafiya, inda zai ma gabatar da makala a wajen taron. Kakakin ya kuma ce Buhari zai bar Najeriya ne ranar Litinin, sannan ana sa ran dawowa