Posts

Showing posts with the label Gadar Sama z Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Bayyana Gamsuwar Da Yadda Aikin Titin Karkashin Kasa Da Gadar Sama A Tul'udu Da Dan Agundi Ke Gudana

Image
Daga Naziru Idris Ya'u Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ake gudanar da ayyukan Tal'udu da DanAgundi na karkashin kasa da gadar sama. Gwamnan wanda aka gan shi cikin farin ciki a lokacin da ya kai ziyarar bazata inda ya yaba da irin ci gaban da aka samu kawo yanzu. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya samu rakiyar sakataren gwamnatin jihar Dr. Abdullahi Baffa Bichi, Sanatan Kano ta kudu Alhaji Abdulrahman Kawu Sumaila, da ‘yan majalisar zartarwa, ya kai ziyarar duba ayyukan da ake gudanarwa. Gwamnan ya mika godiyarsa ga ‘yan kwangilar aikin tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnati ta jajirce wajen ganin an kammala wadannan ayyuka a kan lokaci da kuma inganci. Ya kuma kara jaddada cewa abin da gwamnati ta sa a gaba shi ne walwala da ci gaban al’ummar jihar Kano. Ya samu kyakkyawar tarba daga magoya bayansa da dama wadanda suka daga hannu don nuna godiya da ayyukan da ake gudanarwa. Gagarumin nuna goyon baya...