Posts

Showing posts with the label Fintiri

INEC Ta Bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jahar Adamawa

Image
Hukumar zaɓe a Najeriya ta sanar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Adamawa, wanda ya ƙare cikin taƙaddama. Jami'in sanar da sakamakon zaɓen gwamna na Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen ne da ƙuri'a, 430, 861. Gwamnan mai ci ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri'a, 398, 788. Wannan nasara ta bai wa Fintiri ikon ci gaba da mulkin jihar Adamawa a wa'adi na biyu. Da yammacin Talata ne, jami'in sanar da sakamako, Farfesa Mohammed Mele cikin rakiyar wasu manyan jami'an INEC na ƙasa, ya isa zauren karɓar sakamako da ke Yola, inda ya ci gaba da aikin tattara sakamakon ƙananan hukumomin da suka rage. A ranar 15 ga watan Afrilu ne, hukumar zaɓe ta gudanar da cikon zaɓen cikin wasu rumfuna da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar 20. An sake kaɗa ƙuri'u ne a tashoshin zaɓe 69. Sakamakon zaɓen da aka ƙarasa ya nuna cewa 'yar takarar

Yau INEC Za Ta Taron Gaggawa Kan Zaben Adamawa

Image
A yau Talata Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta gudanar ta taron gaggawa da ta kira kan dambarwar sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa da ya tayar da kura. Daga taron ne za a ji shawarar da INEC ta yanke a game da sakamakon zaben gwamnan, wanda a ranar Lahadi hukumar ta dakatar da tattarawa saboda rikicin da ya dabaibaye shi. A ranar Litinin hukumar ta dakatar da Kwamishinan Zabe (REC) na Jihar Adamawa, Barista Hudu Yunus Ari, saboda ya yi gaban kansa wajen ayyana Sanata Aisha Dahiru Binani ta Jam’iyyar APC a matsayin zababbiyar gwamna, alhali ba a kammala tattara sakamakon zaben ba. Lamarin dai ya yamutsa hazo, amma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda yake neman a zaben a Jam’iyyar PDP, ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, domin INEC za ta dauki matakin da ya dace. Tuni dai Fintiri da PDP da kungiyoyin kare dimokuradiyya suka yi tir da abin da kwamishinan zaben ya yi, inda suka bukaci INEC ta dauki mataki a kan wannan kwamacala. Rikicin zaben ya dauki sabon