Har Yau 29 Ga Watan Afurilu Ce Ranar Karshe Ta Rufe Bizar Maniyyata Hajjn 2024 - Laminu Rabi'u Danbappa
Darakta-Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ne ya sanar da haka a yau yayin da yake duba batun sayar da kujerun aikin Hajji da aka ware wa kananan hukumomi a ofishinsa. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Laminu Rabi’u ya bukaci jami’an alhazai na kananan hukumomi da su yi amfani da kwarewarsu wajen gudanar da aikinsu domin cimma manufofinsu. Bugu da kari, babban daraktan ya yaba da kokarin jami’an alhazan na kananan hukumomin, inda ya bayyana cewa gudunmawar da suka bayar ta taka rawar gani wajen ganin hukumar ta samu nasara. Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya tabbatar da hakan ne a yayin wani zaman nazari da aka yi inda ake tantance adadin kujerun aikin Hajji na kananan hukumomi. Ya jaddada cewa Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta tsaya tsayin daka wajen ganin an samu saukin gudanar da aikin Hajji cikin sauki da lada ga dukkan maniyyata. ...