Posts

Showing posts with the label Sanya Hannu

Najeriya da Saudi Arabiya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan aikin hajjin 2024

Image
A yau 7 ga watan Junairu 2024 ne Najeriya karkashin hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta amince da gudanar da aikin Hajjin bana ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ta shekarar 2024 (1445AH) da ma'aikatar aikin hajji da umrah ta kasar Saudiyya. A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da jama'a da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace bikin rattaba hannun da aka yi a Jeddah ya samu halartar manyan wakilai daga Najeriya karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da Malam Jalal Ahmad Arabi, mai rikon mukamin Shugabancin NAHCON.  Tawagar kasar Saudia ta samu jagorancin Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dr. Taufiq Al-Rabiah.     Kafin rattaba hannu kan yarjejeniyar, Ministocin biyu sun yi wata ‘yar gajeruwar tattaunawa inda Najeriya ta bukaci a kawo karshen matsalar karancin tantuna a Mina tare da neman karin wasu sharuddan da suka dace ga dilolin Najeriya a lokacin jigilar ka

Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Dokar Baiwa Dalibai Rance

Image
Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya rattaba hannu a kan dokar da za ta bai wa daliban manyan makarantu bashi su yi karatu, su biya daga baya. Mamba a rusasshen Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Dele Alake ne ya sanar da hakan ranar Litinin. Ya ce za a rika adana kudaden da za a yi amfani da su wajen aiwatar da shirin ne a lalitar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, kuma za a rika bayar da su ne kawai ga daliban manyan makarantu masu karamin karfi. Kudurin dokar dai, ainihi Kakakin Majalisar Wakilai ta tara, Femi Gbajabiamila ne ya gabatar da shi, kuma ya tsallake karatu na uku ne makonni biyu da suka gabata. Dokar dai ta tanadi bayar da bashi mara ruwa ga daliban manyan makarantu marasa karfi ta hanyar Asusun Tallafa wa Ilimi na Najeriya. (AMINIYA) 

Hajj2023 : Kamfanonin Jiragen Sama na Najeriya, Sun Sanya Hannu kan Yarjejeniyar Jigilar Alhazai

Image
Hukumar alhazai ta kasa NAHCON da kuma kamfanin jiragen saman Najeriya hudu sun amince da jigilar maniyyata zuwa aikin hajjin 2023 daga karshe sun sanya hannu kan yarjejeniyar jigilar alhazai ta 2023 tsakanin bangarorin biyu.  A sanarwar da Mataimakin Daraktan yada labarai na hukumar NAHCON, Mousa Ubandawaki ya fitar, Taron wanda ya gudana a dakin taro na gidan Hajji a ranar Talata, ya samu halartar shuwagabannin kungiyoyin hudu. A nasa jawabin, Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya yabawa kishin kasa da kamfanonin jiragen sama suka sadaukar domin tunkarar kalubalen da rikicin kasar Sudan ke fuskanta.  “Ba mu manta da kalubalen da rufe sararin samaniyar kasar Sudan ya haifar ga aikin Hajjin ku ba; duk da haka, ina so in yi kira ga lamirinku da kishin Æ™asa da ku da kada ku Æ™ara dora wa mahajjata Æ™arin kuÉ—i ko canje-canje”. A jawabansu daban daban, Manajan Daraktan Kamfanin  Jirgin Aero, Kaftin Ado Sanusi ya ce jiragen ba su damu da halin da Alhazan da su