Sabbin Katinan Zabe 13m Muka Buga —INEC
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na bincike kan zargin jami’anta da karbar na goro a aikin rabon katin zabe da ke gudana. Hukumar ta kara da cewa ta buga sabbin katinan zabe miliyan 13 da dubu 868 da 441 bayan kammala aikin rajistar sabbin masu zabe. Da yake sanar da hakan, Kwamishinan INEC na Kasa kan Wayar da Masu Zabe da Yada Labarai, Festus Okoye, ya ce, “Hukumar ta damu bayan samun korafe-korafe kan nuna fifiko a wasu wuraren rabon katin. “Duk halastattun masu rajista na da ’yancin karbar katinsu domin kada kuri’a a ranar zabe a wuraren da suka yi rajista.” Ya ci gaba da cewa, “Don haka wajibi ne Kwamishinonin Zabe su tabbatar babu nuna wariya a rabon katin, tare da hukunta jami’ai masu kunnen kashi. “Domin kawar da shakku, sabbin katunan zabe miliyan 3 da dubu 868 da 441 INEC ta buga da suka hada da na sabbin wadanda suka yi rajista da wadanda suka sauya wurin zabe da kuma wadanda aka sabunta katinsu.” Okoye ya sanar cewa hukumar ta kara lokacin rabon katin zuwa ranar 29 ga ...