Posts

Showing posts with the label Professor Abdallahi Sale Usman

Yadda Farfesa Abdullahi Sale Ya Kawo Sauyi A Harkokin Aikin Hajjin Najeriya - Daga Nura Ahmad Dakata

Image
A wani gagarumin yunkurin kawo sauyi, harkar aikin Hajji na fuskantar  sauye-sauye a karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi Sale Usman, shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON). A cikin kankanin lokaci da aka nada Farfesa Usman, ya kafa sabon ma’auni na kirkire-kirkire, inganta aiki, da rikon amana a tafiyar da ayyukan Hajji da Umrah a Najeriya. Sake Tsara Ayyuka: Daya daga cikin manyan gyare-gyaren da Farfesa Usman ya bullo da shi, shi ne kokarin kawo sauyi kan tantance maniyyata aikin Hajji ta amfani da na’ura. Mahajjata nan gaba kadan za su iya yin rajista ba tare da wata matsala ba ta hanyar da aka samar na yanar gizo, tare da rage cikas da tabbatar da gaskiya. Haka nan,  tsarin yana nuna hakikanin matsayin biyan kudin da maniyyaci da neman biza, da shirye-shiryen tafiya, yana Æ™arfafa mahajjata da mahimman bayanai kamar a tafin hannunsu.   Matakan Rage Farashi: Bisa la'akari da nauyin kuÉ—i da ke kan masu zuwa aikin hajji, Farfesa Usman ya ba da fifiko kan...