Posts

Showing posts with the label Annabi

An kori Farfesa daga aiki saboda nuna zanen hoton Annabi lokacin koyarwa

Image
Jami’ar Hamline da ke birnin Minnesota na Amurka, ta kori wata Farfesa, Erika López-Prater, saboda nuna zanen Annabi Muhammad (S.A.W) yayin da take koyarwa. A cewar rahotanni, wata daliba ce a ajin da take koyarwar ta yi korafi ga hukumar jami’ar. An yi garkuwa da tsohon dan Majalisa a Edo Isra’ila ta ba da umarnin cire tutocin Falasdinu daga gine-ginen gwamnati Dalibar, mai suna Aram Wedatalla, ta shaida wa jaridar makarantar cewa ranta ya yi matukar baci da abin da malamar ta yi. Aram dai wacce ’yar asalin kasar Sudan ce ta kuma ce ba za ta taba yarda ta zauna a cikin duk al’ummar da ba za ta mutunta abubuwan da ta yi amanna da su ba. “A matsayina na Musulma kuma bakar fata, bana tunanin zan taba sakin jiki da kowacce irin al’ummar da ba ta mutunta ni kamar yadda nake mutunta ta,” inji ta. Jaridar New York Times ta Amurka ta rawaito cewa Farfesar mai shekara 42, ta yi katobarar ce yayin wani ajin da take koyar da Tarihi, kodayake ta ce ta yi matukar taka-tsatsan kafin nun