Gwamnatin Kano ta kori 'yan mata biyu daga gidan marayu kan zargin tayar da husuma
Hukumomi a jihar Kano ta kori wasu 'yan mata daga gidan marayu na gwamnatin jihar. Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne saboda 'yan matan ba sa bin ƙa'idar zaman gidan tare da ƙoƙarin tayar da husuma tsakanin marayu da ma’aikata. Sai dai marayun sun ce wasu ma’aikatan gidan ne ke cin zarafinsu ta hanyar ƙoƙarin yin lalata da wasu daga cikinsu. Ma’aikatar harkokin mata da walwalar al‘ummar ta jihar Kano, ta ce ta kori ‘yan matan biyu daga gidan marayun na Nasarawa ne saboda rashin kiyaye ka’idoji da dokokin zaman gidan. Sai dai waɗannan ‘yan mata sun ce saboda sun kwarmata lalatar da ake zargin wani ma’aikacin gidan ne ya sa aka kore su, kamar yadda ɗaya daga cikinsu ta shaida wa Majiyarmu Ta ce ''saboda yana da mabuɗin sito a hannansa, yana ganin kamar shi ke da iko da gidan gaba ɗaya, sai muka je muka gaya wa shugabar gidan, daga baya sai ta zo ta ce ai mun yi masa ƙazafi, daga sai suka rubuta takarda suka kai wa Kwamishina, ita kuma ta bayar da umarnin...