Posts

Showing posts with the label Ma'aikatan Lafiya

Burtaniya Ta Dakatar Da Daukar Ma'aikatan Lafiya Daga Najeriya

Image
Gwamnatin Birtaniya ta dakatar da daukan ma’aikatan lafiya daga Najeriya. Wannan dai na kunshe ne cikin sabuwar dokar daukan ma’aikatan ketare da Gwamnatin Birtaniyar ta yi wa kwaskwarima da ta wallafa a shafinta na Intanet. Da wannan dai a yanzu Najeriya ta shiga sahun kasashen duniya da Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana a matsayin masu bukatar gaggawa ta fuskar karancin ma’aikatan lafiya da za su jibinci lamarin kiwon lafiyarsu. A watan Maris ne WHO ta wallafa sunayen kasashen duniya 55 da ke fama da karancin ma’aikatan lafiya ciki har da Najeriya. Gwamnatin ta Birtaniya ta ce akwai bukatar Najeriya da sauran kasashen da lamarin ya shafa su mayar da hankali wajen bunkasa harkokin kiwon lafiyarsu musamman ta hanyar dakile daukar ma’aikatan lafiyarsu aiki da ake yi a ketare. A ranar Alhamis ta makon jiya ce Majalisar Wakilai ta amince da kudirin da ke shirin tilasta wa likitoci share shekaru biyar a Najeriya kafin samun izinin zuwa kasashen waje aiki. Wani dan Majali