Posts

Showing posts with the label SIyasar Kano

Darussa Daga Siyasar Kano Ta 2023 - Dr Sa'idu Ahmad Dukawa

Image
Tun lokacin da Injiniya Abba Kabir Yusuf ya zama gwamnan Kano daga zaben da aka gudanar a watan Maris na wannan shekarar (ta 2023) har izuwa ranar Laraba, 20/9/23, siyasar Kano (wacce ake yiwa taken “sai Kano!”) ta dada zafafa fiye da ko da yaushe a wannan zubin dimokaradiyyar (ta Jamhuriya ta hudu). A bisa fahimtata, dalilai kamar shida ne suka janyo haka.  Za mu yi bitarsu a takaice domin amfanin gaba. 1. Zafin hamaiyar siyasa tsakanin Senator Rabiu Musa Kwankwaso da Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Wannan ta sa wadannan jagororin na Kano guda biyu sun fifita bukatun kansu, na neman wani ya ga bayan wani a siyasance, fiye da bukatar da Kano take da ita na su hada kansu domin su samarwa da Kano zaman lafiya da cigaba mai dorewa.  A dalilin haka magoya bayansu sun dukufa wajen ganin jagoransu ne a sama ta kowane hali. Don haka cece-kuce ya kazanta a tsakanin juna. Da Allah zai sa idan aka kai karshen tirka-tirkar wadannan manyan biyu su yafewa juna su yi sulhu a tsakani...

Duk wanda ya yake ni Sai ya gane kurensa - Kwankwaso

Image
Dan karar shugaban kasa na Jam’iar NNPP, Sana Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce duk wanda ya yake shi a Jihar Kano a zaben 2023, sai ya yaba wa aya zaki. Jaridar Aminiya ta rawaito cewa Kalaman tsohon gwamnan jihar na zuwa ne bayan gwamna mai ci kuma wanda ba sa ga maciji, Abdullahi Ganduje, ya ce wa magoya bayan Jam’iyyar APC, a 2023 Kano za ta maimaita abin da ta yi a zaben shugaban kasa na shekarar 1993. Ana ganin kalaman na Ganduje tamkar gugar zana ce cewa Kananawa ba za su zabi Kwankwaso ba a zaben da ke tafe a ranar 25 ga waan Fabrairu. Amma a martanin Kwankwaso, ya ce, “Ba na son kula wancan mutumin, ban san ko ya fada ko bai fada ba, amma duk wanda ya yaki NNPP ko Kwankwaso a 2023 sai ya i da-na-sani.” Ya ci gaba da cewa, “Duk wanda ya san ni, ya san abin da na yi a baya, ya san idan na ci zaben shugabna kasa, Kano za ta fi kowa amfana, Arewa za ta amfana, haka kuma kasa baki daya.” A cewarsa, “Kwanan nan yi gangamin yakin neman zabe wadanda ke cikin mafiya kayatarwa, b...

2023: Dalilin Da Ya Sa Muka Tsayar Da Gawuna Takarar Gwamnan Kano– Ganduje

Image
  Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar sun tsayar da Mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin dan takarar Gwamnan jam’iyyar a zaben 2023 ne saboda kwarewarsa. Ya ce biyayya da ilimi da kwarewa da kuma kyakkyawar mu’amalarsa da jama’a su ne suka karfafa zaben nasa. Yana mai cewa, babu wata jam’iyya a Kano da ke da dan takara kwararre irin Gawuna. Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron gidauniyar da abokin Gawuna ya shirya a Abuja. “Dokta Gawuna na sane da shirye-shirye da kuma ayyukanmu, kuma mun yi amannar mutum ne wanda zai taimaka wa cigaban al’uma. “Wannan shi ne irin mutanen da muke raino, wadanda za su yi tsayin daka wajen ci gaba daga inda aka tsaya da kyawawan ayyukan bunkasa al’uma da aka asassa. Inshaa Allah za mu ci gaba da haka. A cewar Ganduje, “Daya daga cikin abubuwan da muka yi la’akri da su shi ne ci gaba da ayyuka saboda muhimmancin hakan a sha’anin shugabannci. “Mun tattara ba...