Ma'aikatar Ilimi Ta Kano Ta Fara Gangamin Wayar Da Kai Kan Shirin Gwamnati Na Ayyana Dokar Tabaci Kan Ilimi.
Yayin Da Tawagar Takai Ziyarar Karaye Da Masarautar Rano A shirye-shiryen ayyana dokar ta-baci kan ilimi a hukumance da gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ma'aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara gangamin wayar da kan jama'a kan sabbin manufofin ilimi. A sanarwar da daraktan wayar kan jama'a na ma'aikatar, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanyawa hannu, yace wata tawaga mai karfi a karkashin jagorancin kwamishinan ilimi na jihar a yau ta ziyarci masarautun Karaye da Rano domin wayar da kan al’ummar yankunan kan shirin gwamnati na ayyana dokar ta-baci kan ilimi. Da yake jawabi a fadar Mai Martaba Sarkin Karaye Dr. Ibrahim Abubakar II, Kwamishinan Ilimi na Jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana cewa a ranar 6 ga Mayu, 2024 gwamnatin jihar Kano za ta kafa dokar ta-baci a fannin ilimi. Kwamishinan ya bayyana cewa da wannan sanarwar, ilimi zai kasance kan gaba, domin bangaren farko da ke samun fifikon gwamnati shi ne ginshikin ci gaban dan Adam. A karkashin wannan ...