Posts

Showing posts with the label Sharada

Gwamnan Kano Ya Sauke Hadimansa Guda Biyu Daga Mukaminsu

Image
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta amince da korar manyan mataimaka biyu (Senior Special Assistants) nan take, bayan samun shaidu masu karfi daga rahotannin kwamitocin bincike da aka kafa kan wasu zarge-zargen aikata laifuka daban-daban. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya fitar a ranar Asabar. A cikin mataki mai tsauri, Gwamna Abba ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, Mai taimaka masa na musammam kan Kan Hada kawunan yan siyasa bayan wani kwamitin bincike na musamman ya same shi da hannu wajen belin wani sanannen dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu, inda shaidar da Sharada ya bayar da kansa gaban kwamitin ta tabbatar da rawar da ya taka a wannan mataki na bayar da beli. A wasikar da Sakataren Gwamnati ya fitar a ranar Juma’a, 8 ga Agusta, 2025, an umarci Sharada da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsa ga Babban Sakataren  na Sashen Bincik...