Shugaba Buhari Zai Zo Kano Gobe Don ƙaddamar da ayyuka Guda 8



Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryen tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari da zai kai ziyarar aiki domin kaddamar da ayyukan raya kasa guda takwas a jihar.
Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Malam Muhammad Garba ya fitar ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai karbi bakuncin shugaban kasar da mukarrabansa.
Ya ce yayin da yake Kano, Buhari zai kaddamar da aikin tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai karfin megawatt 10, Kano a tashar tsandauri ta Dala Inland Dry Port na biliyoyin naira a Zawachiki, karamar hukumar Kumbotso.
Sauran ayyukan sun hada da cibiyar ajiye bayanai ta jihar Kano da ke Audu Bako Secretariat Data da harabar ofis da ke Galaxy Backbone Limited Project a Ahmadu Bello Way.
Sauran kuma an ba da aikin cibiyar kula da cutar daji a asibitin kwararru na Muhammadu Buhari, Giginyu; Gada Mai musayar hannu ta Muhammadu Buhari a Hotoro kan titin Maiduguri da Cibiyar koyar da sana'o'i ta bAliko Dangote dake kan titin Zaria da Rukunin Gidajen Gwamnatin Tarayya dake Gandun Sarki, Darmanawa.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki