An sace gangan man fetur miliyan 17 a Najeriya

 


Wani sabon bincike da aka gudanar kan lamurran da ke wakana a fannin arzikin man Najeriya ya nuna cewar, an fitar da ganga sama da miliyan 17 na danyen mai daga kasar zuwa kasashen ketare ta barauniyar hanya, a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.

Rahoton da Andrew Ogochukwu Onwudili, babban jami’i mai binciken kudi na Najeriya ya fitar, wanda kuma jaridar The Nation da ke kasar ta ruwaito, ya kiyasta cewarkwatankwacin kudin danyan man fetur din da a iya cewa an sace daga kasar ya kai Dala Tiriliyan 1 da biliyan 20, da miliyan 969 da dubu 281.

A cikin rahoton, an tuhumi  Ofishin Akanta-Janar na gwamnatin Najeriya da laifin biyan sama da Naira biliyan 73 ga jami’an da suke tantance inganci da adadin albarkatun mai da isakar gas din da ake shirin fitar da su daga kasar.

Mai binciken yadda ake kashe kudaden Najeriyar ya bayyana cewar, kudaden da aka biya ba tare da an yi  kasafinsu ba, ya saba wa tanadin doka a sashi na 80(4) na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999.

Tsohon babban mai binciken kudi, Adolphus Agughu ne ya sanya hannu kan rahoton, aka kuma mika kundin ga magatakardar majalisar dokokin Najeriya a ranar 29 ga Yuni, na shekarar da ta gabata.

RFI

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki