Bayan Ficewa Daga Tafiyar Tinubu, Naja’atu Ta Koma Wajen Atiku

 


Fitacciyar ’yar siyasar nan ta Jihar Kano kuma daya daga cikin tsofaffin Daraktocin kamfen din dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, Naja’atu Muhammad, ta koma wajen dan takarar PDP, Atiku Abubakar.

Matakin nata na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan ta sanar da ajiye mukamin na Tinubu, tare da ayyana ficewarta daga jam’iyyar mai mulki.

Ta tabbatar da hakan ne yayin ziyarar da ta kai wa Atiku a gidansa ranar Lahadi.

Daga bisani dai ta shaida wa Aminiya cewa yanzu tana goyon bayan takarar ta Atiku a zabe mai zuwa.

A baya dai, Naja’atu, wacce ita ce Daraktar Kungiyoyin Fararen Hula a Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu, ta ce za ta gana da ’yan takarar jam’iyyun siyasa kafin ta dauki matsaya kan wanda za ta mara wa baya.

Ta ce ta dawo daga rakiyar Tinubu ne saboda a cewarta, sam ba ya iya yin tunani da kansa.

Ta ce, “Gaskiya ne yanzu ba na yin Tinubu, dalili ke nan ma da na bar jam’iyyar. Abubuwa da dama sun faru, da kyar yake iya tunani da kwakwalwarsa. Wannan ko shakka babu, mai musu kuma ya je ya nemi bidiyonsa ya kalla.

“Ni ba na la’akari da bambancin addini ko kabilanci a siyasa, shi ya sa tunanina ya fadada. Lokaci ya yi da ya kamata mu ajiye son zuciya mu ciyar da kasarmu gaba. Ba zai yiwu mu ci gaba da tafiya a haka ba. Dalilina ke nan, amma ba ni da wata nifaka a kan kowa,” in ji ta.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki