Posts

Showing posts with the label Kotun Ma'aikata

Labari da dumiduminsa : Kotu ta bada umarnin mayar da Muhuyi Magaji matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano.

Image
Kotun ma'aikata ta kasa da ke zamanta a Kano ta umurci gwamnatin jihar da ta mayar da korarren Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Muhuyi Magaji Rimingado daga kan mukaminsa ba tare da bata lokaci ba. SOLACEBASE  ta rawaito cewa kotun a ranar Talata karkashin jagorancin mai shari’a Ebeye David Eseimo ta yanke hukuncin cewa tsige shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Muhuyi Rimingado daga mukaminsa ya sabawa doka, ba komai bane. Idan dai za a iya tunawa Muhuyi Magaji Rimingado ya maka gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin jihar Kano da kuma babban lauyan gwamnatin jihar gaban kotu suna kalubalantar tsige shi daga mukaminsa. Kotun ta karba kuma ta amsa bukatu da mai da’awar ya yi a kan wadanda ake tuhuma. Ta yanke hukuncin cewa wanda ake kara na biyu ba shi da hurumin bayar da shawarar korar wanda ake tuhuma ba tare da fara sauraren karar ba ta hanyar da ya dace ya kare kansa. Akwai cikakken labarin zai zo muku nan ...

Muhuyi Magaji Ya Karbi Naira Miliyan Biyar Da Dubu Dari Biyar Bayan Da Kotu Ta Tursasa Gwamna Ganduje

Image
Tsohon shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Rimingado, ya karbi kudi naira miliyan 5,713,891.22 daga asusun albashi na gwamnatin jihar Kano. Mista Rimingado ya tabbatar da karbar kudin ne a ranar Alhamis, inda ya ce zai yi amfani da wani bangare na su ne don bayar da agaji. A ranar Talata, kotun ma'aikata ta kasa, Abuja ta umarci GTBank da ya biya Mista Rimingado bashin albashin ma’aikata daga asusun gwamnatin jihar, biyo bayan dakatarwar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi ba bisa ka’ida ba a watan Yulin 2021. Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa gwamnan ya dakatar da Mista Rimingado ne bayan ya bude bincike kan wasu kwangiloli da ake zargin an baiwa wasu kamfanoni masu alaka da iyalan gwamnan. A zaman da aka ci gaba da yi a ranar Talatar da ta gabata, bankin ta bakin lauyansa Joshua Shekwolo ya shaida wa kotun a cikin wata takardar rantsuwa cewa gwamnatin jihar Kano ta na da asusun ajiyar banki da jimillar kudaden da suk...