Posts

Showing posts with the label Alkalai

Kotu A Kano Ta Daure Alkalai Kan Badakalar Kudin Marayu Naira Miliyan 99

Image
Wata Kotun Majistare mai lamba 14 a Jihar Kano ta aike da wasu alkalai da ma’aikatan Hukumar Shari’a gidan gyaran hali saboda zarginsu da wawure Naira miliyan 99. Aminiya ta ruwaito cewa Kotun, karkashin Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti ta aike da mutanen ne bisa zargin su da yin sama da fadi da kudaden wadanda mallakin wasu marayu ne. Tun da farko dai Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ce ta gurfanar da wasu alkalai da kuma ma’aikatan Hukumar Shari’ar Musulunci a gaban kotun. Wadanda aka gurfanar a gaban kotun sun hada da Sani Ali da Sani Uba Ali da Bashir Baffa da Gazzali Wada da Hadi Tijjani Mu’azu da Alkasim Abdullahi da Yusuf Abdullahi da kuma Mustafah Bala. Sauran sun hada da Jaafar Ahmad da Adamu Balarabe da Aminu Abdulhadi da Abdullahi Sulaiman Zango da Garba Yusuf da Bashir Ali Kurawa da kuma Usaina Imam. Takardar karar ta bayyana cewa ana tuhumar alkalan da ma’aikatan shari’ar da laifin hada kai da cin amana da satar Naira m