Posts

Showing posts with the label Kame

Yanzu-Yanzu : Jami'an 'yan sanda sun kama shugaban hukumar zabe na Adamawa da aka dakatar

Image
Hedikwatar rundunar a ranar Talata ta tabbatar da kama kwamishinan zabe na jihar Adamawa Barr. Hudu Yunusa-Ari wanda ya ayyana dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a zaben da aka kammala kwanan nan. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a Abuja ranar Talata. Ya ce: “Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da kama Barr. Hudu Yunusa-Ari, kwamishinan zabe na jihar Adamawa (REC), wanda ake zargin ya bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne ya lashe zaben gwamna a zaben da aka kammala kwanan nan biyo bayan kiraye-kirayen kama shi da bincike da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi. Hukumar zabe (INEC) a bisa zargin tafka kura-kurai a zaben da aka kammala na zaben gwamna a jihar. “Barrister Ari, wanda tawagar ‘yan sanda masu tsare-tsare, sa ido da tantance zabukan ‘yan sanda suka kama a Abuja ranar Talata 2 ga watan Mayu 2023, a halin yanzu yana hannun

An Kama Donald Trump Kan Zargin Aikata Laifuka

Image
An kama Tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump kan zargin aikata laifuka. An kama shi ne ranar Talata yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta Manhattan. An tsare ‘yan sandan da suka yi sanadin mutuwar matashi a Filato ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matar Dagaci da danta a Kano Ana zargin tsohon shugaban ne da biyan wata mai fina-finan batsa, Stormy Daniels toshiyar baki don kada ta yi bayani game da alakar nema a tsakaninsu lokacin da yake takarar shugaban kasa a zaben 2016. Shi ne tsohon shugaban Amurka na farko da aka taba kamawa a tarihin kasar. To sai dai, a lokuta da dama Trump ya musanta zargin. Sai dai Trump ya ce duk wadanan tuhume-tuhumen da ake masa ba komai ba ne face yi wa takararsa ta neman wa’adi na biyu zagon kasa. AMINIYA 

Za Mu Kama Duk Wanda Ya Dauki Makami Ranar Zabe A Kano —’Yan Sanda

Image
  Mataimakin babban sufeto-Janar na ’yan sanda DIG Hafiz Muhammad Inuwa da ke kula da harkokin zaben shekarar 2023 a yankin jahohin Arewa maso Yammacin Najeriya, ya gargadi ’yan siyasa da magoya bayansu, da su kauce wa yin wani abu da zai tada hankulan masu zabe.  DIG Hafiz M. Inuwa ya bayyana cewa shugaban ’yan sanda Usman Alkali Baba ya umarce su, da su gargadi ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki da su ja wa magoya bayansu kunne gabanin zaben da ke tafe a ranar Asabar 18 ga watan Maris 2023. Ya bayyana hakan ne a Jihar Kano, a ci gaba da shirye-shirye da rundunar ke yi na tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu. Ya kara da cewa fatansu, shi ne a yi zabe lafiya a kammala lafiya, ba tare da nuna siyasa da gaba ba. “Duk wani dan siyasa in dai yana son ci gaban Kano, to zaman lafiya shi ne ci gaban, so ake a zauna lafiya. “Kuma na zo da jawabi, in gargade su, Wallahi ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen maganin duk wani da ya nemi ya tada fitina, “Saboda haka ina tabbata

DSS ta kama mutum biyu a Kano kan zargin tayar da rikici

Image
  Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce ta kama wasu mutane biyu da take zargi da tunzura mutane domin tayar da hankali a jihar Kano gabanin zaÉ“en gwamna da na ‘yan majalisun jiha da za a yi a ranar Asabar.   Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter hukumar ta DSS ta ce mutanen sun naÉ—i hoton bidiyo ne da suke bayanan tunzura jama’a a cikinsu, sannan suka riÆ™a wallafa shi a shafukan sada zumunta.   Ta kuma wallafa sunayen Sharu Abubakar TaÉ“ule mai shekara 37 a duniya, da kuma Isma’il Iliyasu Mnagu mai shekara 51 a matsayin waÉ—anda ta kama.   “Cikin waÉ—annan saÆ™onnin masu haÉ—ari, sun nuna jam’iyyar siyasar da suke goyon baya kuma suka yi kira ga magoya bayansu su kai wa abokan hamayyarsu hari duk inda suka gansu.   “WaÉ—anda ake zargin sun yi kira da a kai wa jami’an tsaro hari yayin zaÉ“en gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da za a yi a ranar Asabar. “Wata jam’iyyar siyasa a Kano na barazanar shirya zanga-zanga a sakamakon shirin kai hare-haren,” in ji hukum

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi na kusan naira biliyan biyar

Image
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeroiya NDLEA ta ce ta kama wasu miyagun ƙwayoyi da kuɗinsu ya kai naira biliyan biyar a wani gidan ajiye kayyaki. A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce ta gano tan bakwai na tabar wiwi a jihohin Legas da Borno da Edo da Enugu da Katsina da kuma birnin tarayya Abuja. Hukumar ta ce daga cikin miyagun ƙwayoyin da ta gano sun haɗar da ƙwayar tramadol da yawanta ya kai 3,264,630, da kwalaben kodin 3,490 da wasu ƙwayoyin. Yayin da yake yaba wa jami'an na NDLEA bisa wannan namijin ƙoƙari, shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya yi kira a gare su da su ƙara tsage dantse domin kawo raguwar ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a ƙasar.