Dan China Ya Yi Ikirarin Kashe Wa Marigayiya Ummita Miliyan 60

Dan kasar Chinan nan da ke zargi da kisan budurwarsa, Ummulkusum Buhari (Ummita), Frank Geng Quanrong, ya shaida wa kotu cewa ya kashe wa marigayiyar kudin da yawansu ya kai Naira miliyan 60.

Yayin zaman Babbar Kotun Jihar Kano Mai lamba 16 a ranar Laraba, Geng, ya yi ikirarin cewa ya kashe mata kudaden ne a tsawon shekaru biyun da suka yi suna soyayya.

“Baya ga manyan kudade da na kashe mata, nakan kai ta wuraren cin abinci kamar a otel din Bristol da Central da sauransu.

“Haka kuma na saya mata gida na Naira miliyan hudu da mota ta Naira miliyan 10. Haka kuma na ba ta jarin Naira miliyan 18 don fara kasuwanci baya ga takalma da jakunkuna da na zuba mata a shagon da ta bude na kimanin Naira dubu 500 da kuma atamfofi da lesi na kimanin Naira miliyan daya. Haka kuma na saya mata fili a Abuja inda ta fara ginawa,” in ji dan Chinan

A cewarsa, ya saya mata gwala-gwalai da kimarsu ta kai Naira miliyan biyar.


“Har ila yau, na saya mata wayar hannu kirar iPhone guda biyu da kudindu ya kai Naira miliyan daya da rabi. Haka kuma na ba ta Naira miliyan 6 don karbo satifiket din karatu daga Jami’ar Sakkwato don a lokacin tana sona.


Haka kuma na ba ta Naira miliyan daya da ta hada wutar sola a gidansu,” in ji shi.


A cewar Mista Geng, lokacin da suka fara shirye shiryen aurensu ya saya mata kayan aure da suka hada da atamfofi da lesi da mayafai da kudinsu ya kai Naira miliyan daya da rabi.

Da take sake bayar da shaida a gaban kotun, mahaifiyar Ummulkusum Buhari, wato Fatima Zubairu ta ce ta ga raunuka guda 11 a jikin gawarta.

Shi ma a tasa shaidar, dan sandan da ya gudanar da bincike a ofishin ‘yan sanda na Dorayi, ya shaida wa kotun cewa ya ga wukar da aka kashe Ummita da ita.

Ita ma da take bayar da shaida a madadin Hukumar Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, Dokta Hauwa Ibrahim, ta shaida wa kotun cewa ta sanya hannu ne a takardar rahoton gawar a madadin Shugaban Asibitin.

Daga nan ne Alkalin kotun, Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Janairu don ci gaba da sauraren shaidun masu kariya.

(AMINIYA)


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki