Hanyoyi huɗu da Facebook ya sauya duniya
Dubi hoton da ke sama. Wannan shi ne yadda Facebook, ko kuma The Facebook kamar yadda aka sani a lokacin, ya ke lokacin da Mark Zuckerberg da wasu aminansa suka ƙaddamar da shi daga matsuguninsu na dalibai shekara 20 da suka gabata. Tun daga wannan lokacin, shahararren shafin sada zumuntar na duniya ya sake fasali da yawa. Amma manufarsa ba ta sauya ba: haɗa mutane a Intanet. Da Kuma samun maƙudan kuɗade daga talla. Yayin da dandalin ke cika shekara 20, ga hanyoyi huɗu da Facebook ya canza duniya. TALLA 1. Facebook ya canza harkar sada zumunta Sauran shafukan sada zumunta, irin su MySpace, sun fara aiki kafin Facebook - amma nan take shafin Mark Zuckerberg ya tashi bayan an ƙaddamar da shi a 2004, wanda ke tabbatar da yadda dandali irin wannan zai iya ɗaukan hankali cikin sauri. ASALIN HOTON, MYSPACE Bayanan hoto, Tom shine abokin kowa na farko akan MySpace, wanda Tom Anderson ya ƙaddamar shekara guda kafin Facebook A cikin ƙasa da shekara ɗaya masu amfani da shi sun kai miliyan ...