Gwamnatin Kano Ta Musanta Cin Zarafin Yara A Gidan Marayu
Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahoton zargin cin zarafin yara da wasu jami’anta suka yi a gidan marayu da ke Nassarawa a jihar. Kwamishinar Harkokin Mata da Ci Gaban Al’umma ta jihar, Dakta Zahra’u Muhammad Umar, ta yi watsi da rahoton yayin da ta zanta da manema labarai a ranar “Wasu masu yin barna ne suka hada labarin don bata sunan gwamnatin jihar nan. “Amma abin da ta faru shi ne ba mu da hurumin ci gaba da zama da kuma kulawa da yaran da suka haura shekara 18 a gidan marayu. Doka ma ba ta ba mu wannan damar ba. “An bukaci wasu mutum biyu, Ladidi da Saudat da su bar gidan marayun tun da yanzu sun zama manya.” Jaridar Aminiya ta rawaito cewa kwamishinar Ta bayyana cewa matan biyu, wadda daya daga ciki bazawara ce, dayar kuma na da aure har da ’ya’ya uku, sun ki barin gidan sannan sun shiga yi wa kwamishinar bita da kulli da sauran ma’aikatan don bata musu suna. “Sun shiga gidan rediyon sun yi kazafin cewar ana cin zarafin yara, ana kai su wurare daban-daban ba bisa ka’ida b