Search This Blog

Showing posts with label Makarantu Masu zaman Kansu. Show all posts
Showing posts with label Makarantu Masu zaman Kansu. Show all posts

Friday, 19 September 2025

Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantun masu zaman kansu

Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu da na sa kai ta Jihar Kano (KSPVIB) ta dauki matakin rufe wasu makarantu guda takwas da ke aiki a fadin jihar, bisa dalilai na karya dokoki da kuma sabawa ƙa’idojin gudanarwar hukumar.

A yayinda yake ganawa da manema labarai, Shugaban hukumar Kwamared Baba Umar ya ce rufe makarantun ya zama wajibi saboda karya dokokin kara kuɗin makaranta da rashin yin takardun na izinin gudanarwa.

Wadannan makarantu sun hada da:

1. Prime College Kano – Alu Avenue, Kano

2. Darul Ulum – Hotoro (Ahmad Musa Road)

3. Gwani Dan Zarga College – (Kofar Waika)

4. Awwal Academy – Rimi (Sumaila)

5. Dano Memorial College – (Sumaila)

6. Unity Academy – Wudil

7. Nurul Islam School

8. As-Saif College.

A makon da ya gabata ne shugaban hukumar Baba Umar ya bada wa’adin mako biyu a kai korafin duk wata makaranta mai zaman kanta da ta kara kuɗin makaranta,Inda yace mutane sun bada hadin mai kuma su sun dauki matakin da ya dace na rufe irin wadannan makarantu tare da gurfanar da su gaban kotu.

Shugaban yace a bisa umarnin Kotu,an dakatar da ayyuka a wadannan makarantun har sai abinda alkali ya yanke hukunci akai.

Yace wasu sun ƙara kuɗin makaranta ba tare da amincewar gwamnati ba.

Baba Umar ya kuma ce sun gano matsalar tsaro da rashin isasshen tsari a cikin gine-ginen wasu daga cikin makarantun.

Sai kuma rashin ingantattun kayan aiki da guraben koyarwa da ya dace da ƙa’idar karatun zamani.

Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki ya zama dole ne domin tabbatar da cewa yara na samun ilimi mai inganci, tare da kare iyaye daga karɓar nauyin kuɗaɗen da aka ɗora musu ba bisa ƙa’ida ba.

Ta kuma yi gargadi ga sauran makarantu masu zaman kansu a jihar da su kiyaye doka da ƙa’idojin gwamnati, inda ta ce duk wanda ya ci gaba da karya dokoki, ba za a yi masa rangwame ba.

Daga karshe ya nemi jama’a su cigaba da kai Rahoton duk makarantar da ta saba doka yana mai cewa ba’a kafa hukumar sa domin kuntatawa makarantun masu zaman kansu ba saidai domin dawo da su kan hanya idan sun kauce.

Saturday, 12 August 2023

Gwamnatin jihar Kano ta soke satifiket din duk wasu makarantu masu zaman kansu da ke aiki jihar

KANO FOCUS  ta bayar da  rahoton cewa mai bawa gwamna shawara na musamman akan cibiyoyin sa kai da masu zaman kansu Alhaji Baba Abubakar Umar ne ya bayyana hakan a wani taro da masu mallakin makarantun a ranar asabar.

Umar ya ce, ana sa ran dukkan makarantun za su karbi sabon fom din rajista domin sabunta takardar shedar.

Mashawarcin na musamman ya nanata kudirin gwamnatin jihar na tsaftace ayyukan makarantu masu zaman kansu tare da tabbatar da bin ka'idoji da ka'idoji.

Ya kuma bukaci masu su biya harajin kashi 10 ga gwamnati a daidai lokacin da ya kamata domin ci gaban fannin.

Umar ya kuma ce komawar sa kan mukaminsa na kula da makarantu masu zaman kansu, bai kamata a yi masa kallon barazana ba, domin ba shi da niyyar cin zarafin kowa.

Ya kuma jaddada matsayinsa na daukar matakan da suka dace kan duk wata makaranta mai zaman kanta da aka samu tana so.

Ya bayyana cewa an samar da wata manhaja da za ta magance duk wata damuwa daga gwamnati, masu makarantu, iyaye da ma masu neman aiki a makarantu masu zaman kansu.

Mai ba da shawara na musamman ya kuma ba wa iyaye tabbacin kare muradun su da na 'ya'yansu.

Da yake jawabi a madadin masu hannun jarin, shugaban kungiyar masu makarantu masu zaman kansu na kasa reshen jihar Kano Alhaji Muhammad Malam Adamu, ya bayyana matakin a matsayin abin ban mamaki kuma abin a yaba ne domin zai kara bunkasa harkar ilimi a jihar.

Muhimman abubuwan da taron ya gudana sun hada da kaddamar da wata manhaja ta samar da bayanai na cibiyoyin masu zaman kansu da na sa kai a jihar


Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...