Ni Na Dora Bala A Gwamna, Kuma Ni Zan Sauke Shi – Tsohon Wazirin Bauchi

 


Tubabben Wazirin Bauchi, Muhammadu Bello Kirfi, ya sha alwashin sai ya cire Gwamnan Jihar, Bala Mohammed, daga mukaminsa kamar yadda shi ma ya cire shi daga mukaminsa.

Kirfi ya bayyana haka ne sakamakon tube masa rawani da Masarautar Bauchi ta yi masa a matsayin Wazirin Bauchi.

Masarautar Bauchi ta tube tsohon Wazirin ne saboda abin da ta kira da rashin biyayya ga Gwamnan Jihar.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi, Kirfi ya ce, “Hanyar da na shigar da shi ofis, ta nan zai bi ya fita.

“Ina daya daga cikin wadanda suka tsaya masa ya samu Gwamna, kuma na ji takaicin abin.

“Wannan shi ne iya abin da zai iya yi, ba komai ba ne wannan saboda babu wata riba da nake samu (a matsayin Waziri) a Fadar Sarki.”

Kazalika, Kirfi ya ce Gwamnan ya ci amanar jiga-jigan ‘yan siyasar da suka taimaka masa wajen cin zabe.

Ya ce Bala ya yi fada da kusan baki dayan wadanda suka yi ruwa da tsaki a zaben da ya lashe 2019.

“Na bar wa Allah komai, Shi ne zai yi mana shari’a kan abin da ke tsakanina da shi,” in ji shi.

A wajen jama’ar Bauchi Gwamna Mohammed ke neman a sake zabensa amma ba a wajen mutum guda ba saboda Allah ke ba da mulki ga wanda ya so,” in ji Zainabari

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki