Posts

Showing posts with the label Gwamnan Abia

Yanzu-Yanzu : Kotu Ta Soke Zaben Zababben Gwaman Jam'iyar LP Alex Otti

Image
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta soke zaben zababben gwamnan jihar Abia, Dr Alex Otti da daukacin ‘yan takarar jam’iyyar Labour a jihohin Abia da Kano. Kotun da Mai shari’a M N Yunusa ke jagoranta ta ce fitowar tasu bai bi ka’idojin dokar zabe ta 2022 ba. An mika kwafin hukuncin da kotun ta yanke ga manema labarai a ranar Juma’a. Kotun da ta shigar da kara mai lamba FHC/KN/CS/107/2023 da Mista Ibrahim Haruna Ibrahim ya shigar kan jam’iyyar Labour da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce jam’iyyar Labour ta gaza mika rajistar zama mambobinta ga INEC a cikin Kwanaki 30 kafin zabukan firamarensu ya sa tsarin ya zama mara inganci. “Jam’iyyar da ba ta bi tanade-tanaden dokar zabe ba, ba za a ce tana da dan takara a zabe kuma ba za a iya bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zabe ba; saboda haka, kuri’un da aka baiwa wanda ake kara na 1, kuri’a ce ta bata,” inji alkalin. Idan dai za a iya tunawa INEC ta bayyana Otti na jam’iyyar Labour a matsayin