Shugaba Tinubu Ya Shawarci Gwamnoni Su Yi Da Matakan Da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Kano Ta Yi Wajen Magance Tsadar Kayan Abinci
A yau ne shugaban kasa Bola Tinubu tare da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a fadar gwamnati ya gana da gwamnonin jihohi 36 da kuma ministan babban birnin tarayya Abuja. Taron dai ya cimma matsaya guda domin tinkarar wasu kalubalen da kasar ke fuskanta a halin yanzu, musamman tsadar abinci da rashin tsaro. A sanarwar da mai bawa Shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya sanyawa hanu, yace, bayan tattaunawa mai zurfi shugaban kasa da gwamnonin sun amince da yin aiki tare don magance matsalolin da kuma magance matsalolin tattalin arzikin da 'yan kasar ke fuskanta. Muhimman abubuwan da taron ya kunsa sun hada da: 1. Akan magance matsalar rashin tsaro wanda kuma ke shafar noma da samar da abinci, shugaba Tinubu yayi furuci guda 3. A. Za a dauki karin jami'an 'yan sanda domin karfafa rundunar. B. Shugaba Tinubu ya sanar da Gwamnonin cewa Gwamnatin Tarayya za ta hada kai da su da Majalisar Dokoki ta kasa wajen samar da wata hanya da za ...