Posts

Showing posts with the label Pele

An sanyawa Jarirai fiye da Dari 700 sunan Pele a Peru

Image
Hukumar Kididdigar Kasar Peru ta bayyana cewar a yayin da duniya ke alhinin rasa Pele, gwarzon dan kwallon kafa na karni, sunansa zai rayu a tsakanin yara fiye da 700 ‘yan kasar da aka haifa a karshen shekarar 2022. Jerin sunayen da jami’an kasar ta Peru suka fitar ya nuna cewar, bayan mutuwarsa gwarzon dan kwallon kafar, an rada wa jarirai 738 da aka yi wa rajista a hukumance sunan ko dai Pele, ko King Pele, ko kuma Edson Arantes ko Edson Arantes do Nascimento, cikakken sunan zakaran kwallon kafa na duniya sau uku. A ranar 29 ga watan Disamba Pele ya mutu yana da shekaru 82 a duniya, wanda kuma aka binne shi a ranar Talata. Iyayen yara a kasar Peru dai sun saba rada wa ‘ya’yansu sunayen fitattun mutane da suke kauna walau a cikin ‘yan wasa ko kuma shugabanni kamar yadda RFI ya ruwaito. Wata kididdiga ta nuna cewar a yanzu haka, sunan Cristiano Ronaldo ne aka fi rada wa yaran kasar, wadanda adadinsu ya kai dubu 31 da 538. Messi kuwa na da takwarori jarirai 371 ne a baya bay...

Fitaccen dan kwallon duniya, Pele ya mutu

Image
  Fitaccen ɗan ƙwallon nan na duniya ɗan ƙsar Brazil, Pele ya rasu yana da shekara 82. Pele ya rasu ne a ranar Alhamis 29 ga watan Disamban 2022 bayan ya sha fama da rashin lafiya. A kwanakin baya an yi ta yaɗa labarin ƙarya na rasuwarsa. Ya rasu ne sakamakon cutar kansar ƙaba da kuma cutar ƙoda Ana ganin Pele shi ne ɗan ƙwallon da ba a taɓa samun irin sa ba a duniya, kuma sau uku yana cin gasar kofin duniya wa ƙasarsa Brazil. Ya ci kofin duniya a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1970. A shekarar 2000 ne kuma hukumar ƙwallon ƙafar duniya FIFA, ta ayyana shi a matsayin ɗan ƙwallon ƙarni. Shi ne ɗan ƙwallon da ya kafa tarihin zura ƙwallaye 1,281 a raga a cikin wasanni 1,363 cikin shekara 21 da ya yi yana buga tamaula. Cikin waɗannan har da ƙwallo 77 da ya ci wa ƙasarsa cikin wasanni 92 da ya buga wa Brazil ɗin. An yi wa Pele tiyata a kan yanke masa kansa a hanjinsa a watan Satumban 2021 a Asibitin Albert Einstein da ke Sao Paulo. An sake kwantar da shi a asibiti a watan Nuwamban 2022. Ƴ...