Ramadan: Gwamna Yusuf ya bada tallafin kayan abinci ga ma'aikatan gidan gwamnati
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayar da tallafin kayan abinci na miliyoyin Naira ga ma’aikatan gidan gwamnatin da ke aiki tare a wani bangare na mika musu na watan Ramadan. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi. Sanarwar ta ce nau'ikan kayan da aka rabawa masu matakin albashi na 1 zuwa na 12 sun hada da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50, da katon macaroni, laka na gero guda goma, da kuma kudi N10,000 kowanne. Da yake gabatar da kayayyakin cikin yanayi na musamman, gwamnan ya bayyana godiyarsa ga Allah da ya ba shi damar yin hakan da nufin ganin an samu nasara ga ma’aikatan sa a cikin watan Ramadan mai albarka. “Yau rana ce ta musamman ba a gare ni kadai ba har ma’aikata na a gidan gwamnati domin na fara cika alkawuran yakin neman zabe na na inganta ayyukan jin dadi ga ma’aikatan gwamnati.” Ya bayyana. Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa za a ci