Posts

Showing posts with the label Jirgin Sama

Rano Air Zai Fara Aiki Ranar Lahadi

Image
Daya daga cikin sabbin kamfanonin jiragen sama a kasar, Rano Air, ya ce zai fara aikin zirga-zirga a ranar Lahadi, 7 ga Mayu, 2023. Kamfanin jirgin wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter ranar Alhamis, ya ce gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, zai kaddamar da jirgin da zai tashi daga filin jirgin sama na Aminu Kano. Hukumar gudanarwar kamfanin na Rano Air na sanar da al’umma cewa gwamnan jihar Kano Dr. Umar Abdullahi Ganduje zai tashi da jirgin a ranar Lahadi 7 ga watan Mayu, 2023 a tashar jirgin kasa ta Malam Aminu Kano. Kano karfe 10:00 na safe. Jirgin kasuwanci na Abuja da Kano zuwa garuruwa daban-daban na Najeriya za su fara aiki nan take." Jaridar PlatinumPost ta rawaito cewa Rano Air mallakin hamshakin attajirin dan kasuwa ne kuma hamshakin mai kasuwanci Man Fetur dan asalin Kano, Auwalu Rano, shi ne Shugaban Rukunin kamfanin A.A. Rano. Kamfanin jirgin, wanda aka kafa a shekarar 2019, ya samu lambobi biyar na EMB 145, kuma yana

Dan shugaban kasar Guinea ya sace jirgin sama na gwamnati

Image
An kama daya daga cikin ‘ya’yan shugabaan Equatorial Guinea kan zargin sa da sace tare da sayar da wani jirgin sama mallakin gwamnatin kasar. An tsare Ruslan Obiang Nsue a ranar Litinin, sannan aka yi masa daurin talala kamar yadda kafar talabijin ta kasar ta bayyana. Tun a cikin watan Nuwamban da ya gabata, aka kaddamar da bincike bayan hukumomi sun gano cewa, daya daga cikin jiragen gwamnati mai lamba ATR 72-500 ya yi batan-dabo  a filin jiragen sama na kasa da kasa. A shekarar 2018 ne aka tura wannan jirgin zuwa kasar Spain domin kula da lafiyarsa, yayin da aka zargi Obiang da sayar da shi ga kamfanin Binter Technic, mai kula da lafiyar jirage a Las Palmas da ke tsibirin Grand Canary a Spain din. Jirgin dai na daukar fasinjoji 74 kuma tun a tsakan-kanin shekara ta 1980, kamfanin ATR na hadin guiwa tsakanin Italiya da Faransa ya kera shi. Da ma dai  Equatorial Guine ta yi kaurin suna a fannin cin hanci da rashawa, inda kungiyar Transparency International ta ayyana ta a ma