Posts

Showing posts with the label Pantami

Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, Shi Ne Ministan Da Ya fi Kowanne Nuna Kwazo A Najeriya - Triangle News Media

Image
A ranar 6 ga Mayu, 2023, a birnin Landan na kasar Birtaniya, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) FCIIS, FBCS, FNCS, ya samu lambar yabo ta "Fitaccen Minista" ta Mujallar Triangle.  A sanarwar da mataimaki na musamman ga Ministan kan kafafen sadarwa na zamani, Yusuf Abubakar ya wallafa, an bayar da wannan lambar yabon ne saboda kwazo, aiki tukuru, kyakkyawan jagoranci da kuma kwazon aiki da Farfesa Pantami ya nuna, wanda ke neman sanya bangaren tattalin arzikin na Najeriya a kan turbar ci gaba. A karkashin jagorancin Farfesa Pantami, fannin tattalin arziki na dijital ya sami nasarorin da ba a taÉ“a gani ba a fannonin shiga yanar gizo, fasahar dijital da kasuwanci, haÉ—a dijital, ka'idojin ci gaba, kariyar bayanai da sirri, da Æ™warewar dijital, da sauransu. Minista Pantami da kan sa ya jajirce wajen samar da wasu muhimman kudirori guda biyu na bangaren tattalin arzikin Najeriya, wato Nigeria Startup Act 2022, dokar da

‘Kusan Sau Miliyan 13 Aka Yi Yunkurin Yi Wa Najeriya Kutse Yayin Zaben Shugaban Kasa’

Image
  Gwamnatin Tarayya ta ce akalla sau  12,988,978  aka yi yunkurin yin kutse a shafukan intanet na Najeriya yayin zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisun Tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan da ya gabata. Hare-haren, a cewar gwamnatin an kai su ne daga ciki da wajen kasar, kuma an yi su ne kan shafukan gwamnati, kusan sau 1,550,000 a kullum. Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata. To sai dai ya ce yunkurin kutsen ya yi tashin gwauron zabo zuwa sau 6,997,277, a ranar zaben Shugaban Kasa ta Asabar. “Abin lura a nan shi ne cibiyoyinmu sun sami nasarar toshe dukkan wadannan yunkurin tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar matakin da ya dace a kansu,” in ji Pantami. Ministan ya kuma ce ma’aikatarsa ta kafa wani kwamitin yaki da irin wadannan hare-haren, kuma ya fara aiki ne ranar 24 ga watan na Fabrairu, sannan ya kammala ranar 28. AMINIYA