Posts

Showing posts with the label Zaben Shugaban Kasa

Al'ummar Turkiya za su kada kuri'a a zagaye na 2 na zaben shugaban kasa

Image
  A  karon farko al’ummar Turkiya na shirin kada kuri’a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, bayan koma bayan da shugaba Recep Tayyib Erdogan ya samu da ya hana shi iya lashe zagaye na farko na zaben duk kuwa da tazarar yawan kuri’u. Shugaba Recep Tayyib Erdogan da ke jagorancin Turkiyya tun daga shekarar 2003, wannan ne karon farko da sakamakon zabe ke nuna ya gaza samun kasha 50 na yawan kuri’un da aka kada duk da cewa akwai gagarumar rata tsakaninsa da babban abokin karawarsa. Gabanin fitar sakamakon zaben, shugaba Recep Tayyib Erdogan yayin jawabi gaban dandazon magoya baya, ya bayyana cikakken shirin da ya ke dashi na sake jan ragamar Turkiya zuwa shekaru 5 a nan gaba. Shugaba Recep Tayyib Erdogan.   via REUTERS - MURAT CETINMUHURDAR/PPO Erdogan mai shekaru 69 ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsa mai rajin bin tafarkin addinin Islama ta lashe galibin kujerun Majalisa, sai dai alkaluman da kamfanin dillancin labaran kasar ya wallafa sun nuna Erdogan a matsayin wanda ya...

‘Kusan Sau Miliyan 13 Aka Yi Yunkurin Yi Wa Najeriya Kutse Yayin Zaben Shugaban Kasa’

Image
  Gwamnatin Tarayya ta ce akalla sau  12,988,978  aka yi yunkurin yin kutse a shafukan intanet na Najeriya yayin zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisun Tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan da ya gabata. Hare-haren, a cewar gwamnatin an kai su ne daga ciki da wajen kasar, kuma an yi su ne kan shafukan gwamnati, kusan sau 1,550,000 a kullum. Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata. To sai dai ya ce yunkurin kutsen ya yi tashin gwauron zabo zuwa sau 6,997,277, a ranar zaben Shugaban Kasa ta Asabar. “Abin lura a nan shi ne cibiyoyinmu sun sami nasarar toshe dukkan wadannan yunkurin tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar matakin da ya dace a kansu,” in ji Pantami. Ministan ya kuma ce ma’aikatarsa ta kafa wani kwamitin yaki da irin wadannan hare-haren, kuma ya fara aiki ne ranar 24 ga watan na Fabrairu, sannan ya kammala ranar 28. AMINIYA

Zamu Kalubalanci Zaben Shugaban Kasa - Atiku Abubakar

Image
ÆŠan takarar shugaban Æ™asa na babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, Atiku Abubakar ya ce dole ne kowa ya Æ™alubalanci zaÉ“en da aka yi na ranar 25 ga watan Fabarairu. A taron manema labarai da ya gabatar a Abuja, tsohon mataimakin shugaban Æ™asar ya ce, abin da ya faru a kan zaÉ“en fyaÉ—e ne aka yi wa dumukuradiyya. Atiku ya ce, a tarihin Æ™asar wannan shi ne zaÉ“e mafi muni da aka taÉ“a yi, wanda kuma dama ce ta sake daidaita Najeriya. Amma kuma hukumar zaÉ“en Æ™asar, INEC ta lalata tare da watsa wannan dama da buri na ‘yan Najeriya. ÆŠan takarar na PDP, ya ce zaÉ“en ya kasa kaiwa matsayi da matakin da aka sa rai zai kai. Sannan ya ce lauyoyinsu suna duba lamarin kafin su san matakin da za su É—auka na gaba. Ya ce idan har ya je kotu ba a yi masa adalci ba to zai bar su da Allah. Za mu kawo muku karin bayani a nan gaba. BBC 

Labari da dumiduminsa : INEC Ta Bayyana Bola Tinubu A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

Image
An ayyana Bola Tinubu, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa. Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Mahmood Yakubu ne ya sanar da sakamakon zaben a safiyar yau Laraba. Yakubu ya ce Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726. Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne ya samu kuri’u 6,984,520, yayin da Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP) ya zo na biyu da kuri’u 6,101,533. "Yanzu na sauke nauyin da ya rataya a wuyana a matsayina na babban jami'in dawo da na kasa," in ji shugaban INEC. “Ni, Farfesa Mahmood Yakubu, a nan na tabbatar da cewa ni ne jami’in da zai dawo takara a zaben 2023. An fafata zaben. “Wannan Tinubu Bola Ahmed na jam’iyyar APC, bayan ya tabbatar da ka’idojin doka, an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma an dawo da shi. Yakubu ya kara da cewa za a bayar da takardar shaidar komawa ga Tinubu da karfe 3 na yammacin Laraba.

Yau Ake Rufe Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Image
  Daga karfe 12 na daren yau Alhamis 23 ga Fabrairu, 2023, za a fure yakin neman zaben ’yan takarar shugaban kasa da Majalisun Tarayya da za a gudanar ranar Asabar. Dokar Zaben Najeriya ta haramta yin duk wani nau’in yakin neman zabe ko tallata dan takara daga sa’a 24 kafin ranar zabe. A yayin rubuta wannan rahoton, kusan awa 12 ya rage wa daukacin jam’iyyu da ’yan takara su yi duk abin da za su iya, su kuma rufe yakin neman zabensu, sannan a fafata a akwatunan zabe a ranar Asabar. Jam’iyyu 18 ne ke zawarcin kujerar shugaban kasa bayan kammala wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari na biyu a ranar 29 ga watan Mayu. Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa za a gudanar da zabukan ne a mazabu 1,491 da ke kananan hukumomi 774 da ke jimillar rumufunan zabe 176, 846. ’Yan Najeriya ne za su yi alkalanci a zaben mai mutum miliyan 95.5 da suka yanki katin zabe, wadanda akasarinsu matasa ne, masu shekara 18 zuwa 35, ko da yake kawo yanzu babu alkaluman adadin wadanda suka karbi katin zabensu. ...

A shirye muke don zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasa - Shugaban INEC

Image
Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman ƙanta a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumarsa a shirye take game da zuwa zaɓen zagaye na biyu na shugaban ƙasar idan har ba a samu wanda ya yi nasara a zagayen farko ba. Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kan shirye-shiryen hukumar na tunkarar babban zaɓen ƙasar da ke tafe a Chatham House da ke birnin Landan a Birtaniya. Ya ƙara da cewa a INEC ta yi shirin yiyuwar zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar, kamar yadda take yi a zaɓuka uku da suka gabata. Shugaban hukumar zaɓe ya kuma ce zaɓen ƙasar da za gudanar cikin wannan shekara zaɓe ne na matasan ƙasar. Farfesa Yakubu ya kuma ce rajistar masu kaɗa ƙuri'a ta nuna cewa matasa ne suka mamaye adadi mafi yawa na masu rajistar zaɓen. Shugaban Hukumar ya ce ya ji daɗin yadda mutane suka fito domin karɓar katinan zaɓensu, yana mai cewa fiye da mutum 600,000 sun karɓi katinansu a jihar Legas kaɗai cikin watan da ya gabata. Ya ƙara da cewa a yanzu adadin mas...