Posts

Showing posts with the label Gawuna

Darussa Daga Siyasar Kano Ta 2023 - Dr Sa'idu Ahmad Dukawa

Image
Tun lokacin da Injiniya Abba Kabir Yusuf ya zama gwamnan Kano daga zaben da aka gudanar a watan Maris na wannan shekarar (ta 2023) har izuwa ranar Laraba, 20/9/23, siyasar Kano (wacce ake yiwa taken “sai Kano!”) ta dada zafafa fiye da ko da yaushe a wannan zubin dimokaradiyyar (ta Jamhuriya ta hudu). A bisa fahimtata, dalilai kamar shida ne suka janyo haka.  Za mu yi bitarsu a takaice domin amfanin gaba. 1. Zafin hamaiyar siyasa tsakanin Senator Rabiu Musa Kwankwaso da Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Wannan ta sa wadannan jagororin na Kano guda biyu sun fifita bukatun kansu, na neman wani ya ga bayan wani a siyasance, fiye da bukatar da Kano take da ita na su hada kansu domin su samarwa da Kano zaman lafiya da cigaba mai dorewa.  A dalilin haka magoya bayansu sun dukufa wajen ganin jagoransu ne a sama ta kowane hali. Don haka cece-kuce ya kazanta a tsakanin juna. Da Allah zai sa idan aka kai karshen tirka-tirkar wadannan manyan biyu su yafewa juna su yi sulhu a tsakaninsu da za

Kano: Hukuncin Kotun Korafin Zabe da Darussan da ya kamata 'Yan Siyasa su koya- MS Ingawa

Image
Daga MS Imgawa A ranar Laraba ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke hukunci kan karar da jam’iyyar APC ta shigar kan sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris. Kotun ta yanke hukuncin cewa kuri’u 164,663 na gwamna mai ci, Abba Kabir na NNPP, an same su da rashin sahihancin sakamakon ko dai ba su da tambari ko sa hannun (ko duka) na shugabannin (Pos). Hakan ya haifar da cire kuri'un da aka ce daga jimillar kuri'un da jam'iyyar NNPP ta samu, inda ta bayyana jam'iyyar APC a matsayin wadda ta yi nasara a zaben. Wannan hukunci ya bar batutuwan magana da yawa: 1. NNPP ta dauki lamarin da wasa ko dai saboda murnar nasara ta dauke musu hankali ko kuma sun raina APC da makasudin lamarin. Hakan ya sa ba su dauki lamarin da muhimmanci ba, suka fuskanci ta da katsalandan kamar yadda APC ta yi wanda hakan ya baiwa APC numfashin da ya kama su. 2. A koda yaushe babu cikakken tsarin zabe. Koyaushe za a sami kubuta ga lauyoyin da za s

Labari da dumiduminsa: Kotu ta ayyana Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya ci Gwamnan Kano

Image
Kotun Sauraron zaben kararrakin zaben Gwamnan Kano, a yau Laraba ta ayyana Dr Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya samu nasarar Zaben Gwamna a Kano Zaman Sauraron Shari'ar Wacce aka gudanar ta hanyar manhajar Zoom, ta samu halartar Wakilan dukkanin bangarorin jam'iyyun guda biyu Tun a safiyar wannan rana, magoya bayan jam'iyyun suka taru a wurare Daban-daban domin jiran tsammanin yadda shari'ar zata kasance Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 

Yanzu-Yanzu: Nasiru Gawuna Ya Taya Abba Gida-gida Murnar Lashe zaɓen Gwamnan Kano

Image
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Kuma wanda ya yiwa jam’iyyar APC takarar gwamnan jihar kano a jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya ce ya karÉ“i Kaddarar faÉ—uwa zaÉ“e tare da taya Abba Kabiru Yusuf Murnar lashe zaÉ“en gwamnan Kano. Nasiru Gawuna ya bayyana hakan ne cikin wani sakon murya da yayi bayani na tsawon mintuna biyu, wanda Sakataren yada labaran sa Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24. ” Mun tsammaci Hukumar Zabe INEC zata duba koken da mukai mata na samun kura-kurai a sakamakon zaben da ya gudana, amma a yau 29 ga watan maris ta sake tabbatar da matsayar ta ta hanyar mikawa Abba Kabiru Yusuf Shaidar lashe zabe , don haka mun dauki wannan a matsayin kaddara”. Inji Gawuna   Yace dama ya fada a baya cewa zai karÉ“i Kaddara idan ya fadi zaben don haka yayi kira ga magoya bayan sa da dukkanin al’ummar jihar kano da zu baiwa sabon zaÉ“aÉ“É“en gwamnan hadin kai don ya gudanar da mulkin sa cikin kwanciyar hankali da lumana.   Mataimakin Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah ya kama

2023: Idan Na Zama Gwamna Zan Bawa Kananan Hukumomin 'Yancinsu - Gawuna

Image
Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar  APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi alkawarin baiwa kananan hukumomin jihar ‘yancin cin gashin kansu idan aka zabe shi a matsayin gwamna. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da shirin gidan talabijin na NTA cikin shirin "The Balot". "Ƙananan Hukumomin wani bangare ne na gwamnati kuma su ne matakin kusa da jama'a wanda ke taimakawa hatta ci gaba da rarraba albarkatu da ayyuka". "A matsayina na tsohon shugaban karamar hukumar na san abin da ya shafi gudanar da mulkinta". Lokacin da nake shugaban karamar hukuma, an ba ni cikakkiyar dama nayi  aiki. Hakan ya sa muka samu nasarori da dama don haka idan aka zabe mu a matsayin Gwamna zan mayar da martani kamar yadda Gawuna ya bayyana”. A sanarwar da babban sakataren yada labaransa, Hassan Musa Fagge ya fitar, Gawuna Ya kara da cewa shi ne wanda ya fi cancanta kuma a shirye ya ke ya zama Gwamnan Jihar Kano bayan ya yi aiki

Zabe - Gawuna Ya Taya Zababben Shugaban Kasa Tinubu Murna

Image
Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya taya zababben shugaban kasa Sen.Bola Ahmed Tinubu da mataimakin zababben shugaban kasa Sen.Kashim Shettima murnar nasarar da suka samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar. 25 ga Fabrairu, 2023.   "Ni da kaina da abokina Hon.Murtala Sule Garo ina muku fatan nasara yayin da kuke daukar nauyin sabunta fata tare da addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya kara muku hikima, karfi, jagora da jagora don aiwatar da aikin da aka dora muku".   "Jagaban, kai ne mutumin da ya dace a halin yanzu, nasararka nasara ce ga dimokuradiyya, ka yi aiki tukuru domin samun nasarar jam'iyyarmu ta APC."   "Ka tabbatar da cewa kai dan dimokradiyya ne na gaske wanda ya nuna jajircewa, kishi da sadaukarwa ga hidima da ci gaban kasarmu."   "Mun gode muku bisa jajircewarku da tsayin dakanku domin mun yi imanin cewa kuna da kyakkyawar niyya don cika alk

Muhawarawar 'yan takarar gwamna ta BBC : Kungiyar Global Group Ta Taya Gwamna Ganduje Murnar bisa Kwazon Gawuna

Image
Wata kungiya ta duniya da ta kware wajen tantance muhawarar siyasar ‘yan takara a fadin duniya , Dandalin tantance muhawarar siyasa (PODAF) ta taya gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano murnar kwazon da mataimakin gwamnan jihar kuma dan takarar gwamna na jihar, Nasiru Yusuf Gawuna ya yi a wajen muhawarar yan takarar gwamna da Sashen Hausa na Gidan Rediyon Birtaniya (BBC) ya shirya a Makarantar koyar da harkokin Kasuwancin Aliko Dangote da ke Jami’ar Bayero, Kano, ranar Asabar. A cikin wata wasika da aka aika wa gwamnan kuma mai dauke da sa hannun babban jami’in kungiyar na Najeriya, Mista Johnson Craig, ya bayyana cewa, “Mun gamsu matuka da yadda mataimakin ku, wanda kuma dan takarar gwamna ne na jam’iyyar APC ya yi a lokacin da aka kammala muhawarar zaben gwamna da sashen Hausa na BBC ya shirya." Cikin sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwaman, Malam Abba ya fitar, ta ce Wasikar a wani bangare na cewa, “Kungiyarmu ta ga ya zama dole mu taya mai girma gwa

Gwamna Ganduje ya bayyana Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin Mutum mai Biyayya da Amana

Image
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan a yayin taron yakin neman zaben jam'iyyar APC a kananan hukumomin Sumaila da Takai. Ya kuma bukaci al’ummar kananan hukumomin biyu da su zabi dan takarar gwamna na jam’iyyar APC da abokin takararsa domin dukkansu an gwada su kuma an amince da su. Gwamnan ya bayyana cewa su biyun sun cancanci a zabe su saboda irin nasarorin da suka samu a ma’aikatun gwamnati daban-daban da suka yi aiki a tsawon shekaru. Dakta Ganduje ya yi nuni da cewa Dr. Nasiru Yusuf Gawauna da Alhaji Murtala Garo sun cancanta haka kuma su sukafi da cewa su gajeshi domin ci gaba da ayyuka da shirye-shiryen gwamnati a bangarori daban-daban da Gina dan Adam. Ya kuma bayyana fatansa na cewa ‘yan takarar na da kwarewa wajen fito da manufofi da shirye shirye da kuma aiwatar da karin manufofi da tsare-tsare da suka shafi ci gaban jihar, idan har aka ba su wa’adi a babban zabe mai zuwa. Gwamnan ya yi amfani da damar wajen yin kira ga masu zabe da su kada kuri

2023: Dalilin Da Ya Sa Muka Tsayar Da Gawuna Takarar Gwamnan Kano– Ganduje

Image
  Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar sun tsayar da Mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin dan takarar Gwamnan jam’iyyar a zaben 2023 ne saboda kwarewarsa. Ya ce biyayya da ilimi da kwarewa da kuma kyakkyawar mu’amalarsa da jama’a su ne suka karfafa zaben nasa. Yana mai cewa, babu wata jam’iyya a Kano da ke da dan takara kwararre irin Gawuna. Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron gidauniyar da abokin Gawuna ya shirya a Abuja. “Dokta Gawuna na sane da shirye-shirye da kuma ayyukanmu, kuma mun yi amannar mutum ne wanda zai taimaka wa cigaban al’uma. “Wannan shi ne irin mutanen da muke raino, wadanda za su yi tsayin daka wajen ci gaba daga inda aka tsaya da kyawawan ayyukan bunkasa al’uma da aka asassa. Inshaa Allah za mu ci gaba da haka. A cewar Ganduje, “Daya daga cikin abubuwan da muka yi la’akri da su shi ne ci gaba da ayyuka saboda muhimmancin hakan a sha’anin shugabannci. “Mun tattara bayana

Aminu Alan Waka ya ajiye takarar sa ya fice daga jam’iyyar Sha’aban Sharada

Image
Bayan ficewarsa daga jam’iyyar ADP Shahararren mawakin nan wanda kuma ya shiga siyasa Aminu Ala, ya fice daga Jam’iyyar ADP ta Sha’aban Sharada ya kuma koma jam’iyyar APC. KADAURA24 ta rawaito cewa Alan Waka dai yana daga cikin ‘yan Kannywood da suka shiga tafiyar Sha’aban Sharada, Inda har ma ya rabauta da takarar dan majalisar tarayya na karamar hukumar Nasarawa a jam’iyyar ADP bisa jagorancin Dauda Kahutu Rarara. Jim kadan bayan ficewarsa daga jam’iyyar ADP, Kadaura24 ta gano Alan waka tare da mataimakin gwamnan kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna wanda Kuma shi ne dan takarar gwamnan Kano na Jam’iyyar APC, hakan Kuma ya tabbatar da cewa ya yanke shawarar marawa Gawuna baya.  Hakan dai na alamta cewa Alan Waka ya koma tafiyar jam’iyyar APC Kuma zai marawa takarar Dr. Gawuna bayan maimakon ta Sha’aban Sharada da ya faro. Ku biyo mu nan gaba kadan idan mun tattauna da Aminu Alan zaku ji cikakken bayani kan dalilansa na ficewa daga tafiyar Sha’aban Sharada zuwa APC ta D