Shugaba Buhari ya gargaɗi ƙasashen ƙetare kan zaɓen Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gargaɗi gwamnatocin ƙasashen ketare kan tsoma baki ko katsalanda a harkokin cikin gidan ƙasar musamman a lokutan zaɓe da ke tafe kasa da kwanaki 42.

Majiyarmu ta rawaito cewa Shugaban ya sanar da hakan ne lokacin da yake maraba da sabbin jakadun Switzerland da Sweden da Jamhuriyar Ireland da Thailand da Senegal da Sudan ta Kudu a fadar gwamnati.

Shugaban ya ce Najeriya tana aiki kafada-kafada da kungiyar ƙasashen yammacin Afirka Ecowas domin shawo kan matsalolin tsaro da bijiro da matakan tabbatar da zaɓe mai sahihanci ba tare da katsalanda ga kudin tsarin mulkin kasa ba.

Ko a shekarar da ta gabata sai dai shugaba Buhari ya yi irin wannan gargadi inda yake cewa burinsa shi ne ganin anyi sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Abin da ya faɗawa jakadun
Wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar ta rawaito shugaba Buharin ya gargadin jakadun ketare kan su mayar da hankali kan abin da ya shafesu da dalilan turo su Najeriya, da kuma kawar da kai kan abubuwan da ba huruminsu ba ne.

Buhari ya ce babu shaka dole za a sa ido kan yada zaɓukan Najeriya za su kasance don haka fatansa shi ne ganin wakilan ƙasashen sun mayar da hankali wajen shirya yada ayyukansu zai kasance domin tabbatar da ganin komai ya tafi cikin kwanciyar hankali.

Sannan ya shaida mu su cewa Najeriya tana aiki sosai da Ecowas domin tabbatar da cewa an mututun dokokin kudin tsarin mulki ba wai kowa damar ‘yanci zaɓen abin da yake so.

Ya kuma jadada cewa yana alfahari da farin ciki irin haɗin-kan da ƙasashen ke bai wa Najeriya musamman a fanonin da suka shafi tsaro da yaƙi da rashawa da inganta tattalin arziki da kuma kokarin haɓɓaka shugabanci na gari.

Ya nemi hadin-kan sauran kasashen duniya wajen shawo kan manyan kalubalen Najeriya da yammacin Afirka.


Martanin jakadun
Wakilan ƙasashen da suka gana da shugaba Buharin sun alkawarta mutunta dokoki da taimakawa Najeriya wajen kare muradanta da kuma tabbatar da ganin an yi zaɓe cikin sahihanci.

Sun ce suna sanne da matsayin Najeriya a Afirka baki ɗaya, da matsayarta a siyasar duniya da girman tattalin arzikinta.

Jakadun sun yi wa kasar fatan alheri wajen ganin an yi zaɓen 2023 cikin kwanciyar hankali da cikakken tsaro.

Kwanaki 42 suka saura 'yan Najeriya su fita rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa.

Duk da cewa an dan bayyana fargabar wasu matsaloli da ka iya yiwa zaben tarnaki ko haifar da tsaiko, shugaba Buhari ya jadadda cewa zabukan za su gudana kamar yada aka tsara.

Sannan ita ma hukumar zabe ta yi watsi da raɗe-raɗin da wasu bayanai da aka rinka yaɗawa kan yiwuwar dage zaɓen.

'Yan Najeriya dai yanzu hankali ya karkata domin ganin yada za ta kaya a babban zaɓen da ke shirin riskarsu cikin yanayi na matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro



Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki