Posts

Showing posts with the label Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci

Hajj 2024: Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci Ta Najeriya, Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Shirin Hajin Bana

Image
Majalisar Koli ta addinin Musulunci a Najeriya ta bayyana damuwa a game da babbar barazanar da ke tattare da aikin Hajjin bana ga al'ummar Musulmi a Najeriya. A sanarwar da Farfesa Mansur Sokoto ya wallafa a shafinsa na Facebook, yace, binciken da majalisar ta gudanar kan shirye-shiryen aikin Hajjin na bana ya nuna akwai wagegen giɓi a game da shirye-shiryen. Wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta ce wa'adin da hukumomin Saudiyya suka ɗiba game da kammala duk wani shiri da ya kamata kama daga biyan kuɗin kujera zuwa sauran shirye shirye, akwai yiwuwar zai iya cika ba tare da maniyyatan bana sun san halin da suke ciki ba na ainihin kuɗin da ya kamata su cika kan kujerar. Majalisar ta ce har kawo yanzu ba a biya kuɗin rabin kujerun da aka ba wa Najeriya ba. "Babban abin damuwar shi ne mutanen da suka fara biyan wani daga cikin kuɗin kujerar aikin Hajjin na bana, har yanzu suna cikin rashin sanin inda suka dosa," in ji sanarwar. Daga bisani majalisar ta ce ta...