Posts

Showing posts with the label Kaduna

Bayan Shekara Uku, an sake bude Kasuwar Bacci a Kaduna

Image
Bayan shafe tsawon shekara uku ana gyaran Kasuwar Barci da ke Tudun Wada a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, gwamnatin jihar ta sake bude kasuwar. Ana iya tuna cewa, tsohon gwamnan jihar, Nasiru El-Rufa’i ne ya rushe kasuwar domin zamanantar da ita. Sai dai wannan yunÆ™uri ya fuskanci kalubale, inda ‘yan kasuwar da dama da suka rasa shaguna da jari ke korafin kudin hayar shago da suka ce ya gagare su. Kan haka ne Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Kabiru Yakubu Jarimi, ya shawarci tsofaffin ’yan kasuwar da su nemi ba’asin shagunansu. Shugaban wanda ya samu wakilcin Sakataren karamar hukumar, Abdulrahman Yahaya, ya shawarci ‘yan kasuwar da su yi watsi da shawarwarin masu hana su komawa kasuwar. Ya ce dole ne su koma su nemi hakkin shagunansu tun da sun kasance suna da shaguna a baya a cikin kasuwar. Aminiya

Sojoji Sun Kutsa Ofishin EFCC Dake Kuduna Domin Kubutar Da Abokan Aikinsu

Image
Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu jami'an sojin saman ƙasar suka kutsa ofishinta da ke Kaduna domin ƙwato 'yan uwansu da hukumar ta tare bisa zargin 'karya dokar aikin tsaro'. Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun jami'ain hulɗa da jama'a na hukumar, Dele Oyewale, ta ce a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba jami'an EFCC sun kama wasu mutum biyar da hukumar ke zargi da aikata laifukan da suka shafi zambar kuɗi ta intanet a unguwar Barnawa da ke birnin Kaduna Hukumar ta ce ta kama mutanen ne ba tare da wani tashin hankali ba, daga nan ne kuma wasu mutum shida - da suka haɗar da sojoji huɗu da ɗaliban cibiyar fasahar aikin sojin sama biyu - waɗanda ke wurin a lokaci da aka kama waɗanda ake zargin, suka yi wa ofishin EFCC da ke Kaduna ƙawanya da nufin tilasta sakin mutanen. ''Daga nan ne kuma aka kama su tare da tsare su a ofishin hukumar,...

Gwamnan Kaduna ya fitar da sanarwar murnar samun nasara a kotu

Image
Na yi matukar farin ciki da kaskantar da kai da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke na tabbatar da nasararata a zaben Gwamnan Jihar Kaduna a 2023.  Hukuncin da aka yanke na tabbatar da farin jinin al’ummar jihar Kaduna ne da suka ba ni. Ina yaba wa Kotun bisa tsayuwar dakan da suka yi. Sun wadatar da haqqoqinmu da aiwatar da dimokuradiyyar zaÉ“e. Ina kuma yabawa dan uwana, Hon. Isah Ashiru Kudan saboda tunkarar Kotun domin ya tona masa kokensa. Wannan ya nuna a sarari na imaninsa ga ka'idodin dimokuradiyya da kuma wajabcin wayewa a cikin tafiyar da 'yan wasan siyasa. Ina kira ga Isah Ashiru da 'yan jam'iyyar adawa ta jihar Kaduna da su hada hannu da mu domin kokarin ciyar da jihar mu gaba. Dukkanmu masu ruwa da tsaki ne a PROJECT KADUNA. Ba game da É—aukakar mutum ba ne. Jama'ar mu na son kowa ya tashi tsaye don magance dimbin kalubalen da ke addabar jihar. Idan har aka hada kan ‘yan siyasa, za a rika isar wa al’ummarmu wata alama da ke nun...

Kotu ta bayyana Zaben Gwamnan Kaduna A Matsayin Wanda Bai Kammala Ba

Image
Kotun sauraren kararrakin zabe da ke zamanta a Kaduna ta bayyana zaben gwamnan jihar Kaduna na 2023 a matsayin wanda bai kammala ba. Kotun dai a yayin ci gaba da zamanta a ranar Alhamis din da ta gabata, a yanke hukuncin da ya kai kashi 2:1, ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba tare da bayar da umarnin sake gudanar da wani zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar cikin kwanaki 90. Don haka kwamitin mutum 3 karkashin jagorancin mai shari’a Victor Oviawe, ya bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 24 da ke gundumomi bakwai na kananan hukumomi hudu da suka kunshi masu rajista 16,300. An sanar da hukuncin ta hanyar Zoom bayan alkalan sun kaurace wa zauren taron. Yabo Ku tuna cewa jam’iyyar PDP da dan takararta Isah Mohammed Ashiru ne suka shigar da karar. Ashiru na jam’iyyar PDP yana kalubalantar zaben Uba Sani a matsayin gwamnan jihar Kaduna bisa zargin magudi da magudin zabe, yana mai cewa dan takararta (Isa Mohammed Ashiru) ne y...

El-Rufai Zai Rushe Kamfanoni 9 Mallakar Makarfi

Image
Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, ya soke lasisin mallakar kamfanoni tara na tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Muhammed Makarfi. An kuma shirya rushe kamfanoni tara mallakar tsohon gwamnan Jihar. Aminiya  ta fahimci cewa an kai sanarwar janye  hakkin mallaka ga jami’an kamfanonin da abin ya shafa. Sanarwar ta fito ne daga Daraktan kamfanin rake da ke lamba 11 a Murtala Square, Alhaji Ibrahim Makarfi wanda ya mayar da martani da cewa, “lauyoyinmu za su mayar da martani kan kwace hakkin mallakar kamfanonin”. Sai dai da yake mayar da martani kan soke hakkin mallakar a wani sakon da ya aike wa Sanata Makarfi, ya tabbatar da samun wasikun soke kamfanonin har guda tara. Ya ce, “Akwai babban batu. Muna bukatar ganawa da Ustaz Yunus (SAN) domin mu garzaya kotu don dakatar da gwamnatin jiha; kawai sun aiko mana da takardun soke mallaka guda tara”. Daga cikin kadarorin da abin ya shafa sun hada da filaye guda biyar a Mogadishu, filaye uku a kan titin Kwato, da fili day...

Wani dan ta'adda ya tarwatsa kansa da bam a Kaduna

Image
  Jama'a sun shiga firgici a jihar Kaduna ta Najeriya bayan wani mutun da ake zargin dan ta'adda ne ya tarwatsa kansa da bam a daidai lokacin da jami'an tsaro ke kokarin cafke shi, yayin da gawarsa ta yi kaca-kaca. Lamarin ya faru ne a kan hanyar Ibrahim Haske da ke unguwar Keke a Millenium City a sanyin Safiyar wannan Litinin.  Mutanen da lamarin ya auku a kan idanunsu sun ce, an yi jin karar harbe-harben bindiga da misalin karfe 1 na cikin daren da ya gabata lokacin da jami'an tsaron farin kaya na DSS da sojoji suka dirar wa gidan dan ta'addar da ake zargi. Mutumin ya tarwatsa kansa ne da bam din bayan ya fahimci cewa, jami'an tsaron sun yi masa zobe. Rahotanni sun ce, mutumin ya dauki lokaci yana musayar wuta tsakaninsa da jami'an tsaro kafin yanke shawarar kashe kansa da kansa, yayin da aka gano bindiga kirar AK-47 a cikin gidansa da kuma wasu bama-bamai. PUBLICITÉ Tuni jami'an tsaro suka tafi da matar mutumin da 'ya'yansa bayan y...

Na Fi Karfin Kujerar Minista A Gwamnatin Tinibu - El-Rufa'i

Image
  Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ba zai karba ba, ko an nada Ministan Babban Tarayya ba a Gwamnatin Bola Tinubu da za a rantsar ranar 29 ga wata Mayu da muke ciki. Gwamnan ya yi wannan furucin ne a yayin da ake shirye-shiryen rabon mukamai a sabuwar gwamnatani, inda ake hasashen za a nada shi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ko kuma ministan Abuja. Yakin Sudan: Akwai yiwuwar maniyyata su kara biyan wasu kudin  DAGA LARABA: Zama Da Uwar Miji A Gida Daya: Inda Gizo Ke Saka “Ko an ba ni ministan Abuja ba zan karba ba. Na sha fada cewa ba na maimaita aji, kuma na san akwai matasan suka fi dacewa da kujerar,” in ji shi. Da yake jawabi a wurin taron kaddamar da wani littafi a Abuja ranar Talata, ya bayyana cewa, “Ba zan koma gidan jiya ba. Kai! Tun da na bar Abuja ban sake komawa ba sai a 2016 da aka nada abokin karatuna a matsayin minista, ya bukaci gani na. “Yanzu na tsufa da fita yin rusau, gara a samo matasa masu jini a jika.” Ya ci gaba da cewa, “Nan da kwana...

Sanata Uba Sani Ya Samu Nasarar Zama Gwamnan Kaduna

Image
An bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Sanata Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2023. Jami’in kula da masu kada kuri’a na jihar Kaduna kuma mataimakin shugaban jami’ar Usman Dan Fodio Sokoto, Farfesa Lawal Suleiman Bilbis ne ya bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben. Sani ya samu kuri'u 730,002 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa Isa Ashiru na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 719,196. Dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Jonathan Asake ya zo na uku mai nisa bayan ya samu kuri’u 58,283 yayin da dan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Suleiman Hunkuyi ya samu kuri’u 21,405.

El-Rufai ya yi wa fursunoni 11 afuwa a Kaduna

Image
Gwamnan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya amince da yin afuwa ga fursunoni 11 daga gidajen yarin jihar domin murnar sabuwar shekarar 2023. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwaman kan kafofin yaɗa labarai na gwamnan jihar Mista Muyiwa Adekeye ya fitar. Afuwar ta shafi fursunonin da suka nuna kyakkyawan hali da waɗanda suke fama da rashin lafiya kamar yadda sanarawar ta bayyana. Haka kuma gwamnan ya nemi al'ummar jihar da su ci gaba da kasancewa masu son zaman lafiya, tare da fatan cewa aikin da ya faro tun a shekarar 2015 domin inganta rayukan al'umma jihar za su ci gaba a gwamnati mai zuwa. (BBC HAUSA)