Tinubu Ya Ba Da Umarnin Bai Wa ’Yan Najeriya Tallafi
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin bayar da tallafi domin rage wa ’yan Najeriya domin rage musu radadin cire tallafin mai da Gwamnatin Tarayya ta yi. Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) Mele Kyari ne ya sanar da haka, yana mai cewa biyan tallafin mai da gwamnati ke yi ya zama tarihi, hasali ma ba a ware masa ko sisi ba a kasafin kudi. Da yake bayani bayan ganawarsa da jagororin jam’iyyar APC mai mulki, Kyari ya ce a halin yanzu ma NNPC na bin gwamnati bashin Naira tiriliyan 2.8 da ya kashe wajen biyan tallafin man, don haka kamfanin ba zai iya ci gaba da biya ba. “Har yanzu gwamnati ta kasa biyan Naira 2.8 da muke bin ta, wanda ya isa hujja cewa gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin man ba,” in ji Kyari. Ya bayyana cewa babu wanda zai ba da bashi ga wanda ake bi bashin Naira tiriliyyan 2.8, don haka, kamfanin NNPCL ba zai iya kara biyan tallafin a madadin gwamnati ba. Hasali ma kudin da NNPC ke kashewa wajen biyan tallafin na hana shi sauke nauyin da ya ...