Posts

Showing posts with the label Sauya sheka

Sama da mutum 1,000 'Yan APC Sun Koma Jam'iyyar NNPP

Image
A wani gagarumin sauyi sama da mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 1,000 na jihar Kano suka sauya sheka zuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a ranar Asabar. Mutanen sun fito ne daga kananan hukumomin Shanono da Bagwai, mataimakin gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo a madadin gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya tarbe su a fadar gwamnatin jihar Kano. Wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu ya rabawa manema labarai, ya bayyana jin dadin Gwarzo na karbar wadanda suka sauya sheka. Ya jaddada cewa jam’iyyar NNPP ta ba da fifiko kan hadin kai kuma za a yi wa daukacin mambobinsu adalcin da ya dace. A cewar Garba, mataimakin Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin na aiwatar da shirye-shiryen da za su amfani daukacin jihar Kano, ya kuma bukaci a ci gaba da baiwa gwamnati goyon baya domin ci gaban jihar. Da yake jawabi tun da farko, shugaban masu sauya shekar, Alhaji Haruna Babangida Abbas (Kosashe), ya bayar d