Posts

Showing posts with the label Dalibai

Shafin Karbar Rancen Karatu Zai Fara Aiki Ranar Juma’a —Gwamnati

Image
A ranar Juma’a mai zuwa za a bude shafin neman rancen kudin karatu da Gwamnatin Tarayya ta bude domin dalibai zai fara aiki. Manajan Daraktan Asusun Lamunin Karatu na Najeriya (NELFUND) Mista Akintunde Sawyerr ne ya bayyana 24 ga Mayu, 2024 a matsayin ranar bude shafin neman rancen kudin karatun ga dalibai. Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis. Ya ce masu buƙatar rancen za su iya shiga shafin ta www.nelf.gov.ng domin neman wani agaji kuma sai su tuntubi hukumar asusun ta info@nelf.gov.ng. Ya ce: “Ta shafin, dalibai za su iya samun rance kudin makaranta ba tare da damuwa ba.” Sanarwar da ke dauke da sa hannun mai kula da harkokin yada labarai da hulda da jama’a na asusun, Nasir Ayitogo, ta ce shafin samar da rancen na da saukin sarrafawa kwarai da gaske. Manajan Daraktan Asusun Lamunin karatun Najeriya ya shawarci wadanda suka cancanci wannan tallafi su gaggauta cikewa domin su mori tsarin da zai taimaka wa gobensu. (AMINIYA)

Karin Dalibai 7 Na Jami'ar Kogi Sun Shaki Iskar 'Yanci

Image
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta ce an kuɓutar da ƙarin wasu ɗalibai bakwai da aka sace a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence da ke yankin Osara a jihar Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Williams Aya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis. Aminiya ta ruwaito kamar yadda hukumar ‘yan sandan ta tabbatar cewa an sace ɗalibai 24 a jami’ar kuma zuwa yanzu an ceto 21 daga ciki. Ya ce Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Egbetokun, ya tura ƙwararru domin ci gaba da aikin ceto ragowar ɗaliban da ke hannun masu garkuwa da su. “An tura sashen tsaro na rundunar ‘yan sanda na sama, wanda ya ƙunshi jami’an rundunar masu amfani da jirgi masu saukar ungulu da aka horar da su kan binciken ta sama da jami’an sa ido da kuma sashen leƙen asiri na fasaha (TIU) don ci gaba da aikin ceton da kuma kai farmaki kan masu aikata laifuka a jihar. “Ƙwararru jami’an tsaro tare da haɗin gwiwa ne suka kai ga ceto ƙarin mutane bakwai (7) da a

Gwamna Abba Kabir Ya Kaddamar Da Rabawa Daliban Sakandare JAMB 6,500 Kyauta

Image
Ta hanyar samar da karin damammaki na neman ilimin manyan makarantu a jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf a yau ya kaddamar da rabon fom din JAMB kyauta ga daliban makarantun sakandire 6,500 a wani taron da ya gudana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati Kano. Cikin wata sanarwa da kakakinsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai ya nakalto Gwamnan a lokacin da yake kaddamar da rabon tallafin yana mai cewa, “Yayin da muke raba fom din JAMB kyauta a yau ga ‘yan jihar Kano 6,500, bari na tabbatar da hakan alama ce ta jajircewar gwamnatinmu  alƙawarin saka hannun jari a makomar yaranmu “Mun yi imanin cewa ilimi ginshikin ci gaba ne, kuma idan aka ba wa dalibanmu ilimi, yaranmu za su samu ilimi mai inganci, muna aza harsashin samar da ci gaba mai dorewa a jiharmu ta Kano.” Inji Gwamna Abba. Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen yin karin haske kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu wajen bunkasa fannin ilimi a cikin watanni goma da suka hada da; sake daw

An Sako Daliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ekiti

Image
An sako daliban da malaman nasu ne kimanin mako guda bayan an yi garkuwa da su   Dalibai tara da malamansu da aka yi garkuwa da su a Jihar Ekiti sun kubuta daga hannun ’yan bindiga. Da misalin karfe 2 na dare, kafin wayewar garin yau Lahadi ne masu garkuwa da su suka sako su. Hukumomi a jihar sun tabbatar da sako daliban su tara tare da malamansu. An sako daliban da malaman nasu ne kimanin mako guda bayan an yi garkuwa da su a makarantar Apostolic Faith Group of Schools da ke yankin Emure-Ekiti. Kawo yanzu dai babu bayanin ko an biya kudin fansa. An yi garkuwa da su ne a makarantar Apostolic Faith Group of Schools da ke yankin Emure-Ekiti. (AMINIYA)

Gwamnatin Tarayya ta ce daga watan Satumbar wannan shekara za ta fara ba wa dalibai rance-Mashawarcin Shugaban

Image
Mashawarcin Shugaban Kasa kan Ayyuka na Musamman, Dele Alake, ya kara da cewa gwamnati za ta bullo da sabbin hanyoyin tallafa wa dalibai masu karamin karfi. “Daga cikin abubuwan da gwamnatin ta tsara na tabbatar da ganin kowane dalibi ya kammala karatunsa a kan lokaci, komai karamin karfin iyayensa, akwai daukar su aikin wucin gadi a makarantunsu, bayar da rance da kuma daukar nauyin wadanda suka cancanta a cikinsu,” a cewarsa. Alaka ya ce dokar bai wa dalibai rance da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu za ta fara aiki gabanin shiga sabuwar shekarar karatu mai kamawa a watan Satumba . Sai dai kuma bai ce uffan ba game da matakai ko shirye-shiryen da gwamnatin ta yi domin tabbatar da hakan. Ya kuma  nesanta Gwamnatin Tarayya da karin kudin rajista da sauransu da jami’o’inta suka yi, inda ya ce, har kwanan gobe ba a biyan kudin makaran a jami’o’in, don haka babu gaskiya a rahoton da wasu kafofin yada labarai suka wallafa cewa gwamnatin ta kara kudin makaranta a jami’o’inta. Ya

Gwamnatin Kano Za Ta Biya Wa Dalibai Dubu Hamsin Da Biyar Kudin Jarrabawar NECO

Image
Daya daga cikin manufofin gwamnatin jihar Kano na mayar da bangaren ilimi matsayi na gaba da kuma ba shi kulawar da ake bukata, gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da biyan kudin NECO ga daliban makarantun gwamnati 55,000 nan take domin samun damar tsayawa takara a shekarar 2023 SSCE. A Sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa, gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin kwanaki ashirin da suka gabata a gidan gwamnati. Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bukaci daliban da suka amfana da su yi aiki tukuru don ganin an samu sakamako mai kyau sannan kuma su mayar da hankali wajen ganin sun tabbatar da dimbin jarin da gwamnatin jihar ta yi don gudun kada su daina neman ilimi. A cewar Gwamnan, “A matsayina na gwamnatin da abin ya shafa, mu tabbatar da cewa ba a daina ci gaban karatun ku na neman ilimi ba, kuma nan take na ami

Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Dokar Baiwa Dalibai Rance

Image
Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya rattaba hannu a kan dokar da za ta bai wa daliban manyan makarantu bashi su yi karatu, su biya daga baya. Mamba a rusasshen Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Dele Alake ne ya sanar da hakan ranar Litinin. Ya ce za a rika adana kudaden da za a yi amfani da su wajen aiwatar da shirin ne a lalitar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, kuma za a rika bayar da su ne kawai ga daliban manyan makarantu masu karamin karfi. Kudurin dokar dai, ainihi Kakakin Majalisar Wakilai ta tara, Femi Gbajabiamila ne ya gabatar da shi, kuma ya tsallake karatu na uku ne makonni biyu da suka gabata. Dokar dai ta tanadi bayar da bashi mara ruwa ga daliban manyan makarantu marasa karfi ta hanyar Asusun Tallafa wa Ilimi na Najeriya. (AMINIYA) 

Labari da dumiduminsa : Gwamanatin Kano Za Ta Fara Aikin Tantance Daliban Da Za Ta Dauki Nauyinsu Don Karo Karatu A Kasashen Waje

Image
Gwamnan ya ce "A cikin jawabin da na gabatar ranar rantsuwa, na bayyana cewa mun dawo da tsarin nan na cigaba da bayar da tallafin karatu ga ɗaliban mu na jihar Kano domin samun manyan digiri a cikin gida da ƙasashen waje.  Cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na #Facebook, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da "A cikin watanni masu zuwa, za a fitar da ƙarin bayani, kuma za a fara aikin tantancewa domin fara wannan aiki. Haka kuma, za a buɗe makarantun fasaha guda 44 da Makarantun koyon Ilimin Addinin Musulunci guda 44 da ke fadin kananan hukumominmu da Gwamnatin Sanata Kwankwaso ta kafa, wadanda gwamnatin da ta gabata ta rufe kuma ta yi watsi da su domin ci gaba da karatu da.

An Wajabta Wa Mata Musulmi ’Yan Sakandare Yin Shigar Musulunci A Borno

Image
Gwamnatin Borno ta wajabta yin lullubi ga ’yan mata Musulmai da ke makarantunta na sakandare a fadin jihar.  Daraktan Kula da Makarantu na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Borno, Bukar Mustapha-Umara, ya bayyana cewa, ƙarƙashin sabon tsarin, wajibi ne kowace ɗalibar sakandare Musulma ta sanya wando da riga da ɗankwali da lullubi a duk makarantar da take a fadin jihar. “Wannan shigar ta zama wajibi ga dukkan ɗalibai mata Musulmi a duk makarantunmu na sakandare da ke Jihar Borno. “Amma ga ɗalibai Kirista mata zaɓi ne; In sun so sa su iya kasancewa da shigar da suke da ita a yanzu ko kuma su canza wando kawai.” Tinubu ya gana da Ganduje a Abuja Da sanin Ganduje Tinubu ya gana da Kwankwaso —Kofa Daraktan ya kara da cewa cewa wajibi ne shugabannin makarantun su tabbatar da bin ƙa’idojin sabuwar shigar. Ya kuma bayyana cewa sabuwar dokar sanya tufafin dole ga ɗalibai Musulmi za ta fara aiki daga zangon karatu na farkon shekarar karatu ta 2023/2024 da ke tafe. Sannan ya yi kira ga iyaye