Gwamnatin Kano Za Ta Haɗa Hannu Da Ƙasar Ghana Kan Kiwon Lafiya Da Abubuwan Inganta Rayuwa
Gwamnan jihar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf ya jaddada shirin gwamnatinsa na hada gwiwa da gwamnatin Ghana a fannonin samar da kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa, ilimi da kuma inganta rayuwar jama'a domin amfanin al'ummar Ghana da Kano. A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, Gwamnan ya fadi hakan ne a yau a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin ministan lafiya na kasar Ghana, Mista Mahama Ase Asesini wanda ya jagoranci tawagar jami’an ma’aikatar a ziyarar ban girma da suka kaiwa gwamnan a gidan gwamnati. Alh Abba Kabir Yusuf ya ce ‘yan kasar Ghana da mutanen Kano suna da kamanceceniya da yawa ta fuskar al’adu, addini, al’ada, auratayya da sana’o’i masu dimbin yawa wadanda za a iya kulla su tun shekaru da dama da suka gabata kuma ya bayar da shawarar karfafa dankon zumuncin da aka kulla. Gwamna Abba ya yi amfani da wannan dama wajen sanar da ministar wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu wa