Gwamna Abba Kabir Yayi Ta'aziyyar Rasuwar Marigayi Dr. Faizu Baffa Yola
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar Dakta Faizu Baffa Yola wanda ya rasu a yau (Alhamis) sakamakon rashin lafiya da ya yi yana da shekaru 74 a duniya. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana a cikin wani yanayi na alhini game da gudunmawar da Marigayi Dokta Faizu Baffa Yola ya bayar wajen ci gaban harkokin kiwon lafiya a jihar da kuma wajensa da kuma yadda yake taimakawa bil’adama a kowane lokaci. “Mun samu matukar kaduwa da labarin rasuwar Dr. Faizu Baffa Yola, wani kwararren likita wanda ya shafe tsawon rayuwarsa yana hidima ga al'uma a fannin kula da lafiya da sauran ayyukan jin kai. “Abubuwan alkhairin da ya yi ba zai gushe ba saboda gudunmuwar da ya bayar a ci gaban jihar da kasa baki daya ba za a iya mantawa da shi cikin sauki ba kuma zai zama jagora ga masu son bin tafarki madaidaici. “A madadin gwamnati da na...