Posts

Showing posts with the label WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana karshen annobar Covid-19

Image
A jiya Juma’a ce hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an kawo karshen annobar Covid-19, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da wargaza tattalin arziki da sha’anin zamantakewar duniya, sama da shekaru 3 bayan da ta ayyana ta a matsayin annoba.  Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya sanar da haka a jiya Juma’a, inda ya yi gargadin cewa har yanzu cutar na nan a matsayin barazana. Wannan mataki na hukumar Lafiyar na zuwa ne bayan da kwamitin kwararru mai zaman kansa da ta nada a game da wannan cuta ta Covid ya ce cutar ba a bukatar mayar da hankali sosai a kan cutar daga hukumar. Sai dai a cewar Tedros, hatsarin cutar bai kau ba, inda ya yi kiyasin cewa ta kashe sama da mutane miliyan 20 a fadin duniya, kimanin ninki 3 na mutane kusan miliyan 7 da aka ce ta kashe a hukumance. A ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2020 ce hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana cutar Covid-19 a matsayin annoba, makwanni bayan da ta bulla a birnin Wuhan na kasar China. RFI 

Fiye da kashi 48 na al'ummar Afrika ba sa samun kulawar lafiya- WHO

Image
  Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ‘yan Afrika miliyan 672 wanda ke wakiltar kashi 48 na al’ummar nahiyar basa samun kulawar lafiyar da ya kamata yayinda suke rayuwa cikin cutuka. WHO ta ce dai dai lokacin da kasashe ke baje hajar gagarumin ci gaban da suka samu a bangaren kiwon lafiya, yayin bikin ranar Lafiya ta Duniya har yanzu Afrika na ganin mummunan koma baya a bangaren. Daraktar hukumar WHO shiyyar Afrika Dr Matshidiso Moeti ta ce bangaren kiwon lafiya na ci gaba da samun koma baya a nahiyar wanda ke da nasaba da rashin kulawar shugabanni don habaka sashen. A sanarwar da ta fitar a ranar lafiya ta Duniya wato World Health Day da ke gudana a kowacce ranar 7 ga watan Aprilu, shugabar ta WHO reshen Afrika, ta ce gazawar bangaren lafiya ya haddasa karuwar cutuka a sassan nahiyar da kuma tsanantar cutuka masu hadari. Dr Matshidiso Moeti ta ce abin takaici yadda hatta kananun cutukan da basu kai su yi kisa ba, su ke iya kashe tarin jama’a a nahiyar ta Afrika saboda gurguncewar banga

Mutane biliyan biyar ka iya kamuwa da bugun zuciya a duniya

Image
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, kimanin mutane biliyan biyar na fuskantar gagarumin hatsarin kamuwa da ciwon zuciya saboda cin abinci mai dauke da kitse da ta bayyana amatsayin guba L A shekarar 2018 ne, Hukumar Lafiyar ta Duniya ta yi roko da a kawar da cimakar da ke dauke da kitse ganin yadda mutane dubu 500 suka yi mutuwar-farar-daya a sassan duniya sakamakon wannan cimakar. WHO ta ce, kasashen duniya 43 da ke dauke da jumullar mutane biliyan 2 da miliyan 800, sun dauki matakin daina kalace da irin wannan cimakar a kasashensu, amma har yanzu akwai mutanen duniya kimanin biliyan biyar da aka gaza ba su kariya a sassan duniya. WHO ta ce, Masar da Australia da Koriya ta Kudu, na  cikin kasashen duniya da suka yi watsi da gargadinta duk da cewa, su ke kan gaba a jerin kasashen da aka fi samun masu kamuwa da ciwon zuciya skamakon yawan cin abinci mai kitse. Ana yawan cakuda wannan kitsen a cikin cimaka daban-daban da suka hada da man girki da abincin gwangwani da wasu kunsassun kayan