Shugaba Buhari Yace, Bai Umarci Atoni Janar Da Gwamnan CBN Kan Kin Bin Umarnin Kotu Ba Dangane Batun Tsofaffin Kudi
Fadar shugaban kasa na son mayar da martani kan wasu damuwar da jama’a ke ciki na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai mayar da martani ga hukuncin da kotun koli ta yanke kan batun kudin tsohon naira 500 da naira 1,000 ba, kuma ta bayyana a nan karara da cewa babu wani lokaci da ya umurci Babban Lauyan gwamnati da Gwamnan CBN su bijirewa duk wani umarnin kotu da ya shafi gwamnati da sauran bangarorin. A sanarwar da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce, tunda aka rantsar da shugaban kasa a shekarar 2015, bai taba umurtar kowa da ya bijirewa umarnin kotu ba, bisa akidar cewa ba za mu iya gudanar da mulkin dimokuradiyya ba tare da bin doka da oda ba, kuma jajircewar gwamnatinsa kan wannan ka’ida ba ta canja ba. Bayan zazzafar muhawarar da ake ta yi game da bin doka da oda dangane da halaccin tsohon takardun kudin, don haka fadar shugaban kasar na son bayyana karara cewa Shugaba Buhari bai yi wani abu da