Babban Bankin Najeriya Ya Ce Ya Kashe Dalar Amurka Biliyan 11.42 Don Farfado Da Darajar Naira
Rahoton da babban bankin Najeriya ya fitar a shafinsa na yanar gizo ya ce bankin ya kashe dalar Amurka biliyan 11.42 a cikin watanni 7, daga watan Janairu zuwa watan Yuli na shekarar 2022 domin a farfado da darajar naira. Masana tattalin arziki da kwararru a fannin hada-hadar kudi na ganin wannan kokari da bankin CBN ya yi bai hana matsalar canji tsakanin dalar Amurka da naira ba, hasali ma har yanzu farashin kayan masarufi na karuwa a kasuwanni. Ya zuwa wannan lokacin, ana sayar da dalar Amurka daya a kan naira 750 a kasuwar bayan fage yayin da a banki kuma ake sayar da dalar kan naira 450, bambancin naira 300 kenan tsakanin banki da kasuwar bayan fage. A hirar shi da Muryar Amurka, Umar Garkuwa, daya daga cikin manyan ‘yan canjin kudi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya ce karyewar naira laifin babban bankin kasar ne ba laifin ‘yan canji ba. Garkuwa ya ce matsalolin harkar canji a Najeriya ba kamar a wasu kasashen duniya ba ne, domin lamarin ya zama wata harka da ...