Posts

Showing posts with the label Ladubban tafiya Idi

Abu bakwai da ya kamata ku yi don tafiya sallar Idi

Image
Sallar Idin ƙaramar salla Ibada ce da Allah Ya shar'anta a matsayin kammala Ibada ta azumin watan Ramadan. Sallar Idi na ɗaya daga cikin sunnoni masu ƙarfi a addinin musulunci wadda ake yi sau biyu a shekara wato, ƙaramar salla da babbar salla. Don haka ne ma sallar idin ke buƙatar wasu abubuwa domin yin guzuri a tafiya zuwa masallacin idin. Dakta Muhammad Nazifi Inuwa wani malamin addini ne a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya bayyana jerin abubuwan da ya kamata mutum ya yi kafin tafiya sallar idi. Wankan Idi Wankan Idi ɗaya ne daga cikin wanka na sunnah a addinin musulunci wanda ake yi sau biyu a shekara. Dakta Muhammad Nazifi Inuwa ya ce an so duk mai tafiya masallacin idi ya gabatar da wankan Idi, domin dacewe da sunnah. Dangane da wankan, dakta Nazifi ya ce mutum zai iya yin wanka na soso da sabulu domin tsaftace jikinsa, sannan daga baya kuma sai ya yi wankan idin, domin dacewa da ladan sunnar wankan. Haka kuma malamin ya ce sigar wankan iri ɗaya ne da na saura...