Posts

Showing posts with the label Tallafin Kudi

Gwamnatin Kano Ta Bada Tallafin Riyal 30,000 Ga Alhazai 50 Da Suka Rasa Kudin guzirinsu

Image
Gwamnatin jihar Kano ta bayar da tallafin Riyal 30,000 na kasar Saudiyya ga Alhazanta 50 da suka yi asarar Kudin guzurinsu a kasar Saudiyya. A sanarwar da mai rikon mukamin shugaban tawagar yan jaridu dake kawo rahoton Aikin hajjin bana, Nasiru Yusuf Ibrahim, ya ce Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jiha, Alhaji Laminu Rabiu Danbappa ne ya sanar da hakan a ranar Talata a wata ganawa da manema labarai a birnin Makkah. Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bayyana cewa, bisa ga girmansa ya bayar da amincewar fitar da kudaden a cikin kasafin kudin da hukumar ta yi da nufin tallafa wa wadanda abin ya shafa amma ba don a biya su diyya ba da fatan abin da ya faru zai zama kaffara. Ya kara da cewa wadanda suka ci gajiyar tallafin sun karbi rabin kudaden daga Riyal na Saudiyya 750 zuwa Dalar Amurka 500. A cewarsa babbar wadda ta ci gajiyar tallafin ita ce wata mace daga karamar hukumar Gwale wadda ta yi asarar dalar Amurka 1,000 sannan ta karbi dalar Amurka 500. Da yake zanta