Bayan Zargin Yi Wa Takararsa Zagon Kasa, Tinubu Ya Ziyarci Buhari A Daura
Yan kwanaki bayan ya zargi Gwamnatin Tarayya da kokarin yi wa takararsa kafar ungulu, ta hanyar wasu manufofinta, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a mahaifarsa da ke Daura a Jihar Katsina. Tinubu dai ya sami rakiyar Gwamnan Jihar ta Katsina, Aminu Bello Masari da wasu Gwamnonin APC, yayin ziyarar da daren Juma’a, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar wa Aminiya. Sai dai babu cikakkun bayanai kan ainihin makasudin ziyarar ta Tinubu zuwa Daura. A ranar Alhamis ce Aminiya ta rawaito yadda Tinubu ya yi zargin gwamnati mai ci ta kirkiro matsalar wahalar man fetur da canjin kudin da suka jefa ’yan Najeriya cikin kunci a ’yan kwanakin nan da gangan ne domin ta gurgunta takararsa. Lamarin dai ya yi ta yamutsa hazo a fagen siyasar Najeriya, inda wasu suke zargin akwai alamun baraka tsakanin dan takarar da gwamnatin jam’iyyarsa. Amma Kakakin Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu, Byo Onanuga, ya zargi ’yan adawa da kokarin rur...